Badakallar kudi: Kotu ta tabbatar da tuhumar da ake yiwa tsohon shugaban NIMASA

Badakallar kudi: Kotu ta tabbatar da tuhumar da ake yiwa tsohon shugaban NIMASA

A yau Alhamis ne babban kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta tabbatar da laifin da ake tuhumar tsohon shugaban rikon kwarya na Hukumar da ke kula da jiragen ruwa da kuma bayar da tsaro wato NIMASA, Calistus Obi na karkatar da Naira miliyan 139 mallakar hukumar.

An kuma tabbatar da laifin Alu Dismas, hadimin tsohon shugaban hukumar ta NIMASA, Patrick Ziadeke Akpobolokemi.

Badakallar kudi: Kotu ta tabbatar da tuhumar da ake yiwa tsohon shugaban NIMASA

Badakallar kudi: Kotu ta tabbatar da tuhumar da ake yiwa tsohon shugaban NIMASA
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An roki Buhari ya ajiye Lai Mohammed a karo na biyu

Alkalin kotun, Jastis Mojisola Olatoregun ta dage yanke hukunci a kansu zuwa ranar 28 ga watan Mayu inda ta bukaci a tsare mutanen biyu a gidan yari har zuwa ranar da za a yanke hukuncin.

Hukumar Yaki da rashawa EFCC ta gurfanar da Obi da abokan laifinsa tun a shekarar 2016 bisa zarginsa da hadin baki da karkatar da kudaden da suka kai Naira miliyan 139.

An gurfanar da Obi da sauran mutanen 8 da laifin hadin baki da karkatar da kudaden gwamnati.

Duk da cewa kotun ba ta same su da laifin hadin baki ba, an same su da laifin karkatar da kudaden gwamnati.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel