Kotun zaben Shugaban kasa ta yi watsi da karar da ke neman a dakatar da rantsar da Buhari

Kotun zaben Shugaban kasa ta yi watsi da karar da ke neman a dakatar da rantsar da Buhari

Kotun sauraron karar zaben Shugaban kasa da ke Abuja ta yi watsi da karar da jam’iyyar Hope Democratic Party (HDP) ta shigar wanda ke neman a dakatar da mukaddashin Shugaban alkalan Najeiya, Justis Tanko Mohammed daga rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu.

Majalisar mutum uku karkashin jagorancin Justis J.S. Ikyegh sun bayyana cewa karar bai da inganci.

Dan takarar shugaban kasa na HDP a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, Ambrose Owuru, ne ya shigar da karar a ranar Talata.

Kotun zaben Shugaban kasa ta yi watsi da karar da ke neman a dakatar da rantsar da Buhari

Kotun zaben Shugaban kasa ta yi watsi da karar da ke neman a dakatar da rantsar da Buhari
Source: UGC

Da yake muhawara akan karar, lauyan Owuru da HDP, Emmanuel Njoku, yayi korafin cewa a karkashin sashi na 1 (2), 6 (6) 139, da 239 na kundin tsarin mulkin 1999, suna so kotun ta hana Buhari gabatar da kansa a ranar 29 ga watan Mayu ko kuma a wani rana don rantsarwa ko karbar rantsuwa a matsayin Shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Nagode da baka musuluntar dani ba – Rotimi Amaechi ga Shugaba Buhari

Hakazalika da suke kafa hujja akan sashi na 26 (4) (5) da 138 (1) na dokar zabe na 2010, Owuru da HDP na so kotun zabe ta hana rantsarwar har sai zuwa ranar da za a yi hukunci kan kararsu da ke kalubalantar zaben Shugaban kasa na ranar 23 ga watanFabrairu.

Amma lauyan Buhari, Wole Olanipekun (SAN); lauyan hukumar zabe, Ustaz Usman (SAN) da kuma lauyan APC, Akin Olujimi (SAN) sun bukaci kotu tayi watsi da karar saboda rashin nagarta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel