Dalilin da yasa na bukaci Zainab Bulkachuwa ta janye daga shari'ata - Atiku

Dalilin da yasa na bukaci Zainab Bulkachuwa ta janye daga shari'ata - Atiku

Dan takarar jam'iyyar adawa a zaben shugabancin kasan Najeriya da ya gudana a watan Febrairu, Atiku Abubakar, ya bayyana dalilin da ya sanyashi bukatar shugabar kotun daukaka karar Najeriya, Zainab Bulkachuwa, ta yanje daga shari'ar zaben shugaban kasa.

Atiku da jam'iyyarsa PDP suna kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben, kuma sun bukaci Zainab Bulkachuwa ta jaye da tawagar alkalan da zasu yanke hukunci kan karar duk da cewa ita ce shugabar tawagar.

Sun ce dalilin mika wannan bukatan shine alakar Zainab Bulkachuwa da wani jagoran APC, wanda ya kasance zababben sanata karkashin APC mai wakiltar jihar Bauchi.

KU KARANTA: Fayemi ya lallasa El-Rufa'i a zaben shugabancin majalisar gwamnoni

A jawabinsa, Atiku yace: "Ni da lauyoyi na, bamu bukaci janyewar alkaliya Bulkachuwa don muna zargin halayenta ko kwarewanta bane. Bal ina matukar ganin girmanta saboda rawar da ta taka wajen kare hakkin diya mace."

Dalilin da yasa lauyoyina suka bukaci janyewarta shine kasancewar mijinta zababben sanata ne karkashin jam'iyyar APC, kuma gashi za tayi hukunci kan abinda ya shafi jam'iyyar mijinta."

A ranar Laraba, kotun ta yi watsi da bukatar Atiku da PDP na cewa Zainab Bulkachuwa ta janye saboda ta na iya rashin adalci. Amma duk da haka, Zainab Bulkachuwa ta yanje daga karar saboda kare mutuncin kanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel