Dan takarar gwamnan PDP ya maka IG da AIG a kotu saboda tsare shi

Dan takarar gwamnan PDP ya maka IG da AIG a kotu saboda tsare shi

Sanata Ademola Adeleke ya maka Sufeta Janar na 'Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu a kotu saboda tsare shi da 'yan sanda su kayi a babban birnin tarayya Abuja a ranar 6 ga watan Mayun 2019.

Dan takarar na jam'iyyar PDP a zaben gwamna da aka gudanar a jihar Osun a Satumban 2018 yana bukatar kotu ta kwato masa hakkinsa na dan adam da a babban kotun Jihar Osun kamar yadda lauyansa Kanmi Ajibola ya gabatarwa kotu.

Cikin karar da ya shigar har da mataimakin sufeta janar na 'yan sanda na Zone 11, Me Leye Oyebade da mataimakin kwamishinan 'yan sanda Simon Lough da mataimakin sufritanda, John Faluyi.

Dan takarar gwamnan PDP ya maka IG da AIG a kotu

Dan takarar gwamnan PDP ya maka IG da AIG a kotu
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamna Yari ya yi watsi da jama'arsa ya tare a Abuja - Wani sanata ya yi korafi

A halin yanzu, Adeleke yana kallubalantar nasarar da dan takarar jam'iyyar APC, Adegboyega Oyetola ya yi na lashe zaben gwamnan a jihar Osun.

Ajibola ya ce 'yan sandan sun tsare Adeleke duk da cewa kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umurnin hana kama dan majalisar.

A cikin hukuncin da ya zartas, Jastis S.O. Falola ya haramatawa 'yan sandan kamawa ko tsare sanatan har zuwa lokacin da aka kammala shari'ar da ke gabansa.

Ya yi nuni ga hukuncin da Jastis I.E. Ekwor na kotun tarayya da ke Abuja ya yi na bawa Adeleke izinin tafiyar kasar Amurka a ranar 7 ga watan Mayu domin duba lafiyarsa.

Jastis Falola ya ce hukuncin babban kotun tarayyar ya haramatawa 'yan sanda kama ko tsare wanda ya ke karewa.

An dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 17 ga wayan Yunin 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel