Rundunar yan sanda tayi umurnin kama direbobin mota masu bakin gilashi

Rundunar yan sanda tayi umurnin kama direbobin mota masu bakin gilashi

- Hukumar yan sandan jihar Anambra ta bada umurnin kama direbobin motocin kasuwa masu bakaken gilashi

- Kakakin yan sandan jihar ya ja kunnen mazauna jihar da baki masu shigowa akan yanda motocin kasuwa masu bakaken gilashi ke tafka ta’asa

- Jawabin ya bayyana cewa masu aikata laifi suna amfani ne da motocin kasuwa da adaidaita sahu masu bakaken gilashi da kuma labule a Awka, Onisha, Ekwulobia, Oki da sauran yankuna masu mutane da dama don yi musu fashi

Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Anambra ta bada umurnin kama direbobin motocin kasuwa masu bakaken gilashi.

A wani jawabin da kakakin yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya gabatar, ya sanar da mazauna jihar da baki masu shigowa akan yanda motocin kasuwa masu bakaken gilashi ke tafka ta’asa.

Rundunar yan sanda tayi umurnin kama direbobin mota masu bakin gilashi

Rundunar yan sanda tayi umurnin kama direbobin mota masu bakin gilashi
Source: Depositphotos

Jawabin ya bayyana cewa masu aikata laifi suna amfani ne da motocin kasuwa da adaidaita sahu masu bakaken gilashi da kuma labule a Awka, Onisha, Ekwulobia, Oki da sauran yankuna masu mutane da dama don yi musu fashi.

KU KARANTA KUMA: Rahoto: Iyaye na aurar da kananan yaransu mata don kayan abinci a sansanin yan gudun hijira na Benue

Rundunar ta yi umurnin cewa duk wani direban motar kasuwa, musamman bus da adaidaita sahu da aka kama yana sauke fasinja da bakaken gilashi ko labulayya zai fuskanci hukunci.

Ta umurci mutanen jihar da su kiyayi shiga irin bus da adaidaita sahu masu kama da haka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel