Rahoto: Iyaye na aurar da kananan yaransu mata don kayan abinci a sansanin yan gudun hijira na Benue

Rahoto: Iyaye na aurar da kananan yaransu mata don kayan abinci a sansanin yan gudun hijira na Benue

- Wasu iyaye sun yanke shawarar aurar da kananan yaransu mata saboda kayan abinci a wani sansanin yan gudun hijira da ke jihar Benue

- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da yunwa da cututtuka, musamman cutar gudawa suka bazu a sansanin

- An tattaro cewa daga gwamnatin tarayya har na jihar sun yi watsi da yan sansanin gudun hijiran

Wani rahoto daga jaridar Leadership ya bayyana yadda wasu iyaye suka yanke shawarar aurar da kananan yaransu mata domin samun kayan abinci a sansanin yan gudun hijira da ke Daudu, karamar hukumar Guma na jihar Benue.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da yunwa da cututtuka, musamman cutar gudawa suka bazu a sansanin.

Tuni dai an tabbatar da mutuwar mutane takwas sakamakon cutar yunwa da sauran cututtuka a sansanin.

Rahoto: Iyaye na aurar da kananan yaransu mata don kayan abinci a sansanin yan gudun hijira na Benue

Rahoto: Iyaye na aurar da kananan yaransu mata don kayan abinci a sansanin yan gudun hijira na Benue
Source: Facebook

Shugaban sansanin, Geofrey Torgenga, ya tabbatar da mutuwar a ranar Laraba, 22 ga watan Mayu, inda ya kara da cewa mutanen sun mutu ne cikin watanni biyar. Ya bayyana cewa yan gudun hira na rayuwa ne da taimakon cocina da kungiyoyi masu zaman kansu.

KU KARANTA KUMA: Muhimman ayyukan ibada 10 da ya kamata mai azumi yayi a goman karshe na Ramadana

“Lokaci na karshe da gwamnatin jiha ta kawo kayayyakin abinci sansanin ya kasance a yammacin ranar zaben Shugaban kasa a watan Fabrairu,” Torgenga ya bayyana.

Wasu mazan sun yi amfani da dammar yunwa a sansanin wajen ba iyayen yara biredi da garri don su auri kananan yaransu. Torgenga ya bayyana cewa iyaye da dama sun bayar da auran yaransu mata, wadanda suke a tsakanin shekaru 10 zuwa 14 ga mazajen da za su iya siya masu garri da biredi.

Yace watsi da su da gwamnatin tarayya da na jiha suka yi abun bakin ciki ne ganin cewa iyalai baki daya daga mazaje, mataye da yara na rarrabuwa wajen neman abinci a wajen jama’a da kuma ranakun kasuwa.

Sauran hanyoyin samun kudi da Shugaban sansanin ya lura dashi shine neman itatuwa a daji da ke kewaye da sansanin don siyarwa, hart a kai wasu yan gudun hijira na zuwa bara.

Ya bayyana cewa a kokarin neman abinci ne, wani dan shekara uku, Nani Lorkyaa, ya bata a watan Maris kuma har yanzu ba a gan shi ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel