Yadda aka gano wani Yaro da ya bace bayan shekaru 6 a Najeriya

Yadda aka gano wani Yaro da ya bace bayan shekaru 6 a Najeriya

A wasu shekaru da su ka wuce ne wani Yaro mai suna Samuel Abdulraheem ya bace a gaban gidan su a Garin Kano. Sai bayan shekaru 6 ne aka yi dace aka tsinci wannan Yaro a Garin Ota da ke Legas.

An yi kicibis da Samuel Abdulraheem ne a wani babban coci da ke cikin Garin Legas bayan shekaru. Raheem ya fito ne daga wani babban gida sannan kuma Iyayensa da ‘Yan uwansa Musulmai ne kamar yadda BBC ta rahoto kwanaki.

Firdausi, ‘Yaruwar wannan Bawan Allah ta bayyana cewa babu irin kokarin da ba su yi ba a lokacin da aka sace Kanin na ta, amma Ubangiji bai yi zai fito a lokacin ba. Dangin Yaron dai duk sun cire rai bayan duk sun dauka cewa ya rasu ne.

Wannan Budurwa mai suna Firdausi tace ba ta taba cire tsammanin za ta ga ‘Danuwan ta ba, har wata rana ta tattara ta koma Legas domin ta samu aikin yi bayan ta kamalla karatu. A nan ne tayi dace ta sake haduwa da ‘Danuwan na ta.

Firdausi wanda ta koma Kirista a Legas ta ke cewa wata rana ta je ibadar nan da Kiristoci su ka saba yi na ‘Shiloh’ a cocin Canaanland da ke Garin Ota, sai ta ci karo da Samuel. Ta hadu da Samuel ne yana yi wa wasu Makafi jagora su na bara.

KU KARANTA: Manoman Kano sun karbi aron Miliyan 900 sun dawo da Miliyan 50 da kyar

Yadda aka gano wani Yaro da ya bace bayan shekaru 6 a Najeriya

Hoton Samuel Abdulraheem da mutanen gidan su
Source: Facebook

Samuel Abdulraheem mai shekaru 13 a Duniya lokacin bai iya tuna cewa an taba sace sa, abin da ya sani kurum shi ne ya zo Legas shekarun baya a jirgin kasa inda aka mika sa wajen wata mata da ta ke tura su bara duk rana tana samun kudi.

Abdulraheem yana ganin cewa an yi masa asiri ne domin bai taba marmarin gida ba. Abin da kurum ya sani shi ne yayi wa Mabarata jagora, ya ci abinci yayi barci, washegari kuma ya sake cigaba da wannan rayuwa da ya samu kan-sa a ciki.

Bayan dogon lokaci ne wannan Matashi ya iya gane ‘Yar uwar sa, daga baya dai Firdausi ta dauke sa ta maida shi gida. Bayan ya dawo cikin hayyacinsa kuma aka fara neman makarantar da za a kai sa bayan yayi shekaru yana yawon bara.

Daga baya aka dace aka sa shi makarantar da ke cikin wannan coci na Canaanland inda ya samu ya kammala Firamare bayan shekarunsa sun soma ja. Daga nan ya zarce Sakandare har ta kai ya shiga jami’ar ABU Zaria kafin a kore sa.

An kama Abdurraheem ne da laifin rubutawa wani abokinsa jarrabawa. Yanzu haka dai yana aiki ne tare da wasu ‘yan kwangila inda ya ci burin komawa karatu a makaranta da zarar ya samu hali a rayuwa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel