Kaka kara kasa: Kwana daya bayan kammala rantsar da Buhari, Igbo suma za suyi ta su rantsuwar

Kaka kara kasa: Kwana daya bayan kammala rantsar da Buhari, Igbo suma za suyi ta su rantsuwar

- Shugabannin kungiyar kabilar Igbo na kasa, sun bayyana ranar 30 ga watan Mayu a matsayin ranar demokuradiyyar yankin

- Sun bayyana rana ce da za su fito kwansu da kwarkwatarsu domin tunawa da shugabannin su da aka kashe lokacin yakin basasa na Biafra

Shugabannin kungiyar kabilar Igbo na kasa wato (Ohanaeze Youth Council) a turance sun bayyana ranar 30 ga watan Mayu a matsayin ranar demokuradiyyar su.

Hakan ya biyo bayan wata sanarwa da fitar ga manema labarai a garin Owerri, wacce shugaban kungiyar na kasa, Igboayaka .O. Igboayaka da kuma sakataren kungiyar na kasa, Chinonso Alozie, suka sanyawa hannu.

A cewar su, ranar za ta zama rana ta tattaunawa game dacigaban tattalin arzikin yankin Igbo, sannan kuma rana ce da suke kira ga dukkanin 'yan kabilar na gida dana waje domin su yi aiki wurin kawo cigaban yankin.

Kaka kara kasa: Kwana daya bayan kammala rantsar da Buhari, Igbo suma za suyi ta su rantsuwar

Kaka kara kasa: Kwana daya bayan kammala rantsar da Buhari, Igbo suma za suyi ta su rantsuwar
Source: UGC

Sanarwar ta ce: "Ranar 30 ga watan Mayu ba wai kawai rana ce da kowa zai zauna a gida ba, rana ce da zamu fito mu tuna da shugabannin mu da suka mutu lokacin yakin basasa na Biafra da kuma wadanda suka yi gwagwarmayar kawo cigaba a yankin mu, sannan kuma rana ce da zamu zauna mu tattauna akan hanyoyin da zamu kawo cigaba ga yankin mu.

"Sabodaa haka kungiyar kabilar Igbo ta kasa tana kira ga dukkanin gwamnonin yankin Igbo da su dauki ranar 30 ga wata a matsayin ranar demokuradiyyar kabilar Igbo.

KU KARANTA: Saraki, Obi, Secondus, sunyi kira ga shugaban kasa ya sanya dokar ta baci a kasar nan

"Sannan muna kira ga dukkanin Sanatoci da 'yan majalisar wakilai na kabilar Igbo, da su zo mu hadu domin kawo cigaba ga yankin mu.

"Mu kabilar Igbo, mun yarda cewa mune muke da mutane mafi rinjaye a nahiyar Afirka, kuma mune muke da kashi 48.9 cikin 100 na al'ummar kasar nan, saboda haka mun bayyana ranar 30 ga watan nan a matsayin ranar demokuradiyya ga al'ummar kabilar Igbo.

"A karshe, zamu yi amfani da wannan damar mu nemi gwamnatin tarayya ta bamu hakuri akan kashe matasan kabilar Igbo guda 1,000 da aka yi a garin Asaba, a lokacin yakin basasa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel