Anyi taho mu gama tsakanin Yansanda da tsagerun Biyafara, 2 sun mutu, 15 sun jikkata

Anyi taho mu gama tsakanin Yansanda da tsagerun Biyafara, 2 sun mutu, 15 sun jikkata

An samu hatsaniya tsakanin jami’an Yansandan Najeriya da tsagerun kungiyar tawaye ta MASSOB dake rajin samar da kasar Biyafara, yayin da suke shirye shiryen bikin cika shekaru 19 da kafa kungiyarsu a karkashin jagorancin Ralp Uwazuruike.

Rikici ya kaure tsakanin bangarorin biyu ne unguwar Iweka dake garin Onitsha na jahar Anambra a ranar Laraba, 22 ga watan Mayu, inda Yansanda suka bude ma tsagerun wuta, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu, tare da jikkata wasu guda goma sha biyar.

KU KARANTA: Kashe kashe: Akalla Sakkwatawa da Zamfarawa 20,000 sun yi gudun hijira zuwa Nijar

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban shiyya na BIM-MASSOB, Amadi Ifeanyi yayin da yake jawabi ga manema labaru a garin Onitsha yana cewa don me Yansanda zasu bude musu wuta bayan ba makamai suke dauke dasu ba.

“Muna shirye shiryen kafa tutarmu a Iweka da misalin karfe 2 na dare ne sai Yansanda suka kewayemu a cikin motoci guda uku, inda suke bude mana wuta, nan take mutanenmu guda biyu suka fadi matattu.

“Anan suka kama yaranmu guda goma, bayan sun jikkata wasu harbin bindiga su goma sha biyar. Sunayen wadanda suka kashe mana sune; Okoye da Uche Ezinwanne, don haka muna kira a sako mana gawarsu.” Inji shi.

Shima daraktan tsaro na kungiyar, Chuks Nnaedozie ya bayyana wasu daga cikin wadanda Yansanda suka raunata, Clifford Nwankwo, Ndubuisi Ikpeazu, Aloy Ibeh da sauran wadanda basu samu sunayensu na har lokacin tattara wannan rahoto.

Daga karshe shugaban BIM-MASSOB na shiyyar Arewacin Onitsha, Christian Emeka ya bayyana cewa akwai yaronsa guda daya da basu san inda ya shiga ba tun lokacin da Yansanda suka kamashi, sa’annan yace babu abinda zai hanasu cigaba da gwagwarmayar kafa kasar Biyafara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel