Saraki, Obi, Secondus, sunyi kira ga shugaban kasa ya sanya dokar ta baci a kasar nan

Saraki, Obi, Secondus, sunyi kira ga shugaban kasa ya sanya dokar ta baci a kasar nan

- Shugabannin jam'iyyar PDP sunyi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanya dokar ta baci a kasar nan saboda matsalar tsaro da ake ta fama dashi

- Sunyi kiran ne a jiya a lokacin da suke gabatar da taron gwamnonin jam'iyyar PDP na kasa a Abuja

Shugaban majalisar dattawa na kasa, Sanata Abubakar Bukola Saraki, Kakakin majalisar wakilai na kasa, Yakubu Dogara da kuma mataimakin shugaban kasa a babbar jam'iyyar adawa ta PDP, Mista Peter Obi, sun gabatar da taro tare da sababbin gwamnonin da suke jiran gado na PDP a Abuja.

Taron wanda aka yi shi a dakin taro na masaukin bakin jihar Gombe, dake Asokoro, majiyarmu ta samu rahoton cewa sun tattauna akan matsaloli da dama, sannan kuma sun tattauna akan sabon shugaban gwamnonin jam'iyyar.

Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, wanda ya jagoranci taron, zai sauka daga shugaban gwamnonin jam'iyyar a mako na gaba, yayin da wa'adinsa zai kare.

Saraki, Obi, Secondus, sunyi kira ga shugaban kasa ya sanya dokar ta baci a kasar nan

Saraki, Obi, Secondus, sunyi kira ga shugaban kasa ya sanya dokar ta baci a kasar nan
Source: UGC

Mutanen da suka samu halartar taron sun hada da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus; Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson; Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom; Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel; Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa da kuma Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal.

Bayan haka kuma, gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson zai karbi ragamar jagorancin gwamnonin daga gurin gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo.

KU KARANTA: Buhari: Zan yi biyayya akan kowanne irin hukunci kotu ta yanke a kaina

Da yake magana da manema labarai, jim kadan bayan kammala taron nasu, Dankwambo ya bayyana Dickson a matsayin wanda zai gaje shi.

A karshen taron, gwamnonin jam'iyyar PDP sunyi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sanya dokar ta baci akan rashin tsaro a kasar nan, duk da cewa suna ta sukar yadda ake kashe al'umma da sace wasua fadin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel