Buhari: Zan yi biyayya akan kowanne irin hukunci kotu ta yanke a kaina

Buhari: Zan yi biyayya akan kowanne irin hukunci kotu ta yanke a kaina

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a shirye yake da ya bi duk wani umarni da kotu ta bashi, akan karar da jaam'iyyar PDP ta shigar a kanshi

- Ya ce ba tun yanzu ba yana girmama fannin shari'a na kasar nan, saboda sau uku yana zuwa gabansu kafin ya zama shugaban kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana girmama fannin shari'a na kasar nan saboda haka zai bi duk umarnin da kotu ta bashi a kowanne irin lokaci.

Dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawa ta PDP Alhaji Atiku Abubakar, shine ya kai shugaban kasar kotu akan cewa a zaben da aka gudanar na shugaban kasa a watan Fabrairu an tafka magudi, kuma yana so kotu ta bi masa hakkinsa.

A lokacin da yake bayani a lokacin shan ruwa da wasu masu fada aji na gwamnatin kasar nan, jiya Laraba a gidansa, Buhari ya bayyana cewa ya yarda cewa kotu za ta yi gaskiya a shari'ar, kuma ya bayyana yadda ya dinga zirga-zirgar zuwa kotu har sau uku a lokacin da yake kokarin zama shugaban kasa.

Buhari: Zan yi biyayya akan kowanne irin hukunci kotu ta yanke a kaina

Buhari: Zan yi biyayya akan kowanne irin hukunci kotu ta yanke a kaina
Source: Twitter

"Ina mutukar ganin girman bangaren shari'a a kasar nan. Saboda sai dana zo gabanku har sau uku kafin na zama shugaban kasar nan. Maganar ku ce ta karshe, idan kuka yi babu wani sauran canji kuma," in ji shi.

Buhari ya yaba da kwarewar alkalan Najeriya, inda yake cewa "kwarewar ku ce ta sanya ake ganin girman ku."

KU KARANTA: Matsalar tsaro ce babbar kalubalen gwamnatin shugaba Buhari - Malamin Addinin Musulunci

A bayanin shi na godiya da kiran shan ruwa da shugaban kasar yayi musu, Alkalin Alkalai na kasa, Ibrahim Tanko Mohammed, ya tabbatarwa da al'ummar kasar nan cewa kotu za ta cigaba da yin iya bakin kokarinta wurin ganin ta dawo da martabar kasar nan a fannin siyasa.

Ya kuma yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da yadda ya nuna halin ko in kula a shari'ar da ake yi dashi a kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel