Boko Haram ta kai harin da yayi sanadiyar rai guda da kuma batar mutum 6 a sansanin soji dake Gubio

Boko Haram ta kai harin da yayi sanadiyar rai guda da kuma batar mutum 6 a sansanin soji dake Gubio

-Harin Boko Haram ya kashe soja daya tare da daidaita wasu shida daga cikin sojin a sansaninsu dake karamar hukmar Gubio ta jihar Borno.

-Buratai ya yabawa mayakan sannan ya basu tabbacin cewa zasu samu karin kayan yaki domin fafatawa da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Hafsun sojin Najeriya Laftanal Janar Tukur Buratai yayi alkawarin samar da isassun kayan aiki ga jami’ansa dake yaki da kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar nan tare da ma sauran dake fada da ta’addanci iri daban daban.

Buratai yayi wannan furucin ne ranar Talata a Borno inda ya kai ziyara ga sansanin soji dake Maiduguri babban birnin jihar.

Boko Haram ta daidaita wani sansanin soji sakamakon farmakin da ta kai

Boko Haram ta daidaita wani sansanin soji sakamakon farmakin da ta kai
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Babu abinda gwamnoni zasu iya akan matsalar tsaro, inji Ishaku

Wata majiyar ta shaida mana cewa, kungiyar Boko Haram ta kai farmaki sansanin soji dake karamar hukumar Gubio a yammacin ranar Lahadi, inda ta kashe soja daya yayin da 6 suka bata ba’a san inda suke ba a yanzu.

Duk da cewa jami’an sojin sun kara da yan kungiyar domin rage munin wannan hari, hakika rahotanni sun nuna cewa jami’an soji 6 sun bata ba’a gansu ba har zuwa daidai lokacin da ake hada wannan rahoto.

Wakilin jaridar Punch yayi naziri akan dalilin da ya sanya Buratai ya ziyarci sansanin sojin, cewa ba don komi ya ziyarcesu ba sai domin ganin cigaban da aka samu fannin yaki da kungiyar Boko Haram da kuma ISIS a yankin.

A wani zance da ya fito daga hannun kakakin rundunar sojin Najeriya, Kanal Sagir Musa, yayi kira ga jami’an sojin da su cigaba da yin ayyukansu akan yadda dokar kasa ta tanada. Kuma su kasance masu jajircewa yayin gudanar da wannan yaki da suke. Ko shakka babu za’a samu karin kayan aiki zuwa gareku.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel