Harin Jihar Akwa Ibom yayi sanadiyyar mutuwar Bayin Allah

Harin Jihar Akwa Ibom yayi sanadiyyar mutuwar Bayin Allah

Jama’a da dama ne su ka rasu a wani mummunan hari da aka kai a wani kauye da ke cikin jihar Akwa Ibom kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Trust Ranar Laraba 22 ga Watan Mayu.

Wasu ‘yan bindiga ne su ka kai farmakai a wani Kauye mai suna Ikot Adaba da ke cikin Garin Oku Iboku a karamar hukumar Itu. Wannan abu ya faru ne a safiyar Ranar Talata 21 ga Watan Mayu.

Wadannan ‘yan bindiga sun iso Kauyen na Ikot Adaba ne a cikin manyan kwale-kwale inda su ka shiga budawa Bayin Allah da ke su da kuma saide-saide a gefen hanya wuta ta ko ina babu kaukautawa.

Wannan Kauye na Ikot Adakpab yayi kaurin suna tun asali da kamun kifi da kuma noma. ‘Yan bindigan sun iso Kauyen ne a daidai lokacin da ake fara shirin cin kasuwar Ranar Talatar da ta wuce.

KU KARANTA: Kashe-kashe: Buhari yayi dogon zama da Masari a Abuja

Majiyar mu ta bayyana mana cewa ana zargin wadanda su ka yi wannan aika-aika sun fito ne daga can yankin Ikot Offiong a cikin Kuros-Riba. Wani mutumin Garin Oku Iboku ya bayyana wannan.

Har yanzu dai ba a iya gano gawar ko mutum guda ba, amma ana cigaba da bincike kamar yadda rahoto ya zo mana. Shugaban karamar hukumar Itu watau Etetim Onuk, ya tabattar da wannan.

Jami’an Soji da ke cikin wannan Kauye ne dai su ka kawo saukin harin bayan sun shiga budawa wadannan ‘yan bindiga wuta. Wannan ya sa Miyagun su ka tsere bayan ganin abin na nema ya fi karfin su.

Wani jami’in Sojoji da ke cikin babban birnin Uyo, Kyaftin SS Jatau da kuma Supol Temino wanda shi ne babban jami’in ‘dan sandan da ka karamar hukumar Itu sun ziyarci inda abin ya auku.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel