Tafka magudi: Shugaban INEC na jahar Bayelsa ya fada hannun Yansanda

Tafka magudi: Shugaban INEC na jahar Bayelsa ya fada hannun Yansanda

Rundunar Yansandan Najeriya ta samu nasarar kama shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, reshen jahar Bayelsa, Pastor Monday Tom Udoh tare da wasu jami’an hukumar guda biyu bisa zarginsu da tafka magudin zabe a yayin babban zaben 2019.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sauran jami’an da Yansandan suka kama sun hada da shugaban INEC na karamar hukumar Nembe, Jude T Nabie da mataimakiyarsa Doris Asiayei.

KU KARANTA: Kashe kashe a Katsina: Buhari yayi doguwar ganawa da Masari a fadar shugaban kasa

Wasu majiyoyi daga sakatariyar INEC ta jahar Bayelsa sun bayyana cewa da fari sai da aka garzaya da Udoh zuwa babban ofishin Yansandan jahar Bayelsa, inda aka umarceshi ya katabta abinda ya sani game da zargin da ake masa, sa’annan aka bada belinsa, daga bisani kuma aka tasa keyarsa zuwa Abuja.

Daga cikin zarge zargen da ake yi ma Udoh da jami’an INEC guda biyu akwai yin karan tsaye ga dokokin zabe, hadin baki, da kuma canza rahotannin yadda zabe ya kasance a kananan hukumomi na magudin zaben da aka tafka a yayin zaben shugaban kasa dana yan majalisu.

Haka zalika wata majiya daga INEC tace Mista Udoh ya tilasta ma turawan zabe wajen sauya rahotannin da suka rubuta game da gaskiyar abin daya faru a rumfunan zaben da suka gudanar, inda ya nemi su rubuta bayanan karya a rahotonsu.

Majiyar ta kara da cewa babu ruwan kotun sauraron korafe korafen zabe cikin wannan lamari, Yansanda kawai suna binciken laifukan da Udoh da jami’an biyu suka aikata ne don ganin doka ta hukuntasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel