Wike ya bayyana abin da ya sa yake marawa Femi Gbajabiamila baya a 2019

Wike ya bayyana abin da ya sa yake marawa Femi Gbajabiamila baya a 2019

Mai girma Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana dalilinsa na goyon bayan ‘dan takarar APC a zaben majalisar wakilan tarayya watau Femi Gbajabiamila duk cewa shi Gwamnan yana PDP.

Nyesom Wike yayi wannan bayani ne a Ranar Laraba 22 ga Watan Mayu. Wike yace cancantar Femi Gbajabiamila ta sa yake tare da shi a zaben majalisar kasar ba wai la’akari da akidar siyasa ba.

Gwamnan ya fadawa jirgin yakin neman zaben na Gbajabiamila da Wase wannan ne a lokacin da su ka kawo masa ziyarar ban girma a gidan gwamnatin jigar Ribas din da ke cikin Garin Fatakwal.

Gwamna Wike yake cewa

‎”Ba na goyon bayan ka saboda ra’ayin siyasa, sai dai don ka cancanci ka rike wannan kujera nake goyon bayanka a zaben majalisar da za ayi.”

KU KARANTA: Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi yana bayan Gbajabiamila

Wike ya bayyana abin da ya sa yake marawa Femi Gbajabiamila baya a 2019

Gwamna Wike ya ajiye siyasa a gefe ya goyi bayan Femi Gbajabiamila
Source: Depositphotos

Gwamnan ya kara da cewa:

“Idan ka samu darewa kan wannan kujera, dole mu hadu mu yi wa Najeriya aiki a matsayin ‘Yan kasa. Jam’iyya wata silar samun mukamin siyasa ce ba komai ba …”

‘Yan majalisun da ke tare da Gbajabiamila da kuma Wase su na yawon kamfe ne a yankin Kudu maso Kudu da kuma bangaren Kudu maso Gabashin kasar, inda jam’iyyar PDP ta ke da karfi sosai.

Har wa yau, gwamnan na Ribas ya koka da yadda sabanin siyasa ya hana Najeriya cigaba:

“Banbancin siyasa ne ya sa Najeriya ta tsaya cak, wannan ne kuma dalilin da ya sa aka ki sa hannu a dokar canza tsarin zabe...”

Fiye da ‘yan majalisa 100 ne ke tare da Femi Gbajabiamila a wannan zagaye da ake yi a cikin Kudancin Najeriya domin ganin ‘dan majalisar na yankin Legas ya gaji kujerar Rt. Hon. Yakubu Dogara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel