Majalisarmu ta baiwa Buhari goyon bayan da ya dace, inji Dogara

Majalisarmu ta baiwa Buhari goyon bayan da ya dace, inji Dogara

-Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya samu lambar girma sakamakon gudanar da kyakkyawan shugabanci a majalisarsa.

-Dogara ya yi ikirarin cewa majalisarsu ba'a taba tamkarta ba tun daga 1960 har zuwa yau.

Kakakin majalisar wakilai ta kasa, Yakubu Dogara yace majalisar dokoki ta 8 a karkashin jagorancinsa ta baiwa gwamantin shugaba Buhari goyon bayan da ya kamata.

Dogara yayi wannan furucin ne jiya a babban birnin tarayya Abuja, jim kadan bayan da wata kungiya ta musamman ta karramashi da lambar girma saboda jajircewarsa wurin yin jagoranci mai inganci a majalisar.

Majalisarmu ta baiwa Buhari goyon bayan da ya dace, inji Dogara

Majalisarmu ta baiwa Buhari goyon bayan da ya dace, inji Dogara
Source: UGC

KU KARANTA:Ku zauna a gida ko ku dandana kudar ku, hukamar ‘yan sanda ta gargadi kungiyar IPOB

Shugaban kwamitin kula da al’adu da kuma dabi’u na majalisar wanda shi ne ya karbi wannan lambar girma a madadin kakakin yace, tabbas Dogara ya cancanci a yaba masa bisa namijin kokarin da yayi na rike wannan majalisa tsawon shekara hudu.

Kazalika, an karrama kakakin ne a dalilin rashin bata lokaci wurin isar da kudurin saukaka yin kasuwanci ga yan Najeriya da sauran kudurorin da suka zo gaban majalisarsa wanda da dama daga cikinsu a yau dokar kasa ta aminta da su.

Bugu da kari, ya yabawa majalisa ta 8 a matsayin wacce ta fi shahara a tarihin Najeriya tun daga shekarar 1960 kawo yanzu saboda akwai lokacin da majalisar dokokin ke aikawa majalisar zartarwa kuduri bayan zama biyu ko kuma a cikin mako guda kacal.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel