Kotu: Atiku zai bukaci Onochie ta biya sa Biliyan 2 na bata masa suna

Kotu: Atiku zai bukaci Onochie ta biya sa Biliyan 2 na bata masa suna

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar zai karasa kotu da wata daga cikin Masu ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara inda zai yi karar ta da laifin ci masa mutunci.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Punch a jiya Laraba 22 ga Watan Mayu, Alhaji Atiku Abubakar zai nemi Lauretta Onochie ta biya sa kudi har Naira biliyan 2 na cin zarafin sa da tayi.

‘Dan takarar shugaban kasar na PDP a zaben bana ya nemi Hadimar shugaban kasar ta ba shi hakuri bayan ta jefe sa da laifin hayar ‘yan ta’adda, amma ta gaza neman afuwarsa domin ya yafe mata.

Onochie ta yada wani labari ne a shafin ta na Facebook inda tace Atiku yana aiki da manyan ‘yan ta’addan Duniya don haka ake nemansa bayan sunansa ya shiga cikin jerin ‘yan ta’adda a kasar UAE.

KU KARANTA: Atiku Abubakar zai shiga Kotu da wata daga cikin Hadiman Buhari

Kotu: Atiku zai bukaci Onochie ta biya sa Biliyan 2 na bata masa suna

Mai ba Shugaba Buhari shawara za ta shiga Kotu da Atiku Abubakar
Source: UGC

Wannan ya sa Lauyoyin ‘dan siyasar su ka ba Hadimar ta Buhari shawara ta janye kalaman ta kuma ta ba Atiku hakuri. Lauretta Onochie ba tayi wannan ba har lokacin da aka ba ta ya kure mata.

Lauyan Atiku watau Mike Ozekhome ne ya bayyana wannan inda yace za su bukaci Onochie ta biya ‘dan takarar na PDP kudi Naira biliyan 2 ko kuma abin da ya haura hakan domin ya rage zafi.

Mike Ozekhome SAN yake cewa a maimakon Hadimar shugaban kasar ta nemi afuwa, sai ta buge da wasu surutai da su ka kara jefa ta cikin matsala. Ozekhome yace Onochie ta debo ruwan dafa kan

Har yanzu dai ba a iya jin ta bakin Lauretta Onochie domin ta kare kan-ta. Su kuwa Lauyoyin Atiku Abubakar sun sha alwashin ganin kotu ta koyawa Hadimar shugaban na Najeriya hankali.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel