Gwamna El-Rufai zai baiwa yara marasa galihu dubu 145 ilimin boko kyauta a Kaduna

Gwamna El-Rufai zai baiwa yara marasa galihu dubu 145 ilimin boko kyauta a Kaduna

Gwamnatin jahar Kaduna a karkashin jagorancin Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai tare da hadin gwiwar babban bankin duniya sun kammala tsare tsaren sanya kananan yara almajirai da kuma yara marasa galihu guda dubu dari da arba’in da biyar a makarantun Boko.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar ilimi ta bai daya ta jahar Kaduna, Nasir Umar ne ya bayyana haka a yayin wani taron kara ma juna sani a Kaduna, inda yace wannan tsari zai fara aikine a watan Satumbar bana.

KU KARANTA: Babbar Kotu a Najeriya ta tsayar da ranar 3 ga watan Oktoba domin gurfanar da Allison Madueke

Gwamna El-Rufai zai baiwa yara matasa galihu dubu 145 ilimin boko kyauta a Kaduna

Gwamna El-Rufai zai baiwa yara matasa galihu dubu 145 ilimin boko kyauta a Kaduna
Source: UGC

Nasiru yace daga cikin kananan yaran basa zuwa makaranta su 727,000 a jahar Kaduna, gwamnati da bankin duniya zasu kwashi yara 145,000 domin mayar dasu aji daya, aji biyu da kuma aji uku a matakin Firamari daga satumbar bana zuwa shekarar 2020.

Daga cikin dalibai 145,000 da zasu mori wannan tsari akwai almajirai dubu goma sha hudu da dari bakiwa da talatin da takwas (14,738) da kuma mata dubu saba’in da dari da sittin da bakwai (70,167) sai kuma makarantu 480 da sabbin malamai 2,420 da za’a dauka aiki.

Bugu da kari shugaban UBEC yace za’a fara gwajin wannan tsari a kananan hukumomi goma sha biyu daga cikin ashirin da uku na jahar ne, kananan hukumomi hudu daga kowanne shiyya.

Haka zalika gwamnati zata raba ma daliban kayan makaranta, littafai, jakkuna, takalma, tabarma, safuna da kuma sauran kayan karatu duka kyauta, daga karshe ya tabbatar da cewa a yanzu haka wani kaso na kudin na kasa, lokaci kawai ake jira a kaddamar da tsarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel