Kashe kashe a Katsina: Buhari yayi doguwar ganawa da Masari a fadar shugaban kasa

Kashe kashe a Katsina: Buhari yayi doguwar ganawa da Masari a fadar shugaban kasa

A ranar Laraba, 22 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari zuwa fadar shugaban kasa dake Abuja domin tattaunawa game da tabarbarewar tsaro a jahar Katsina, tare da lalubo hanyar shawo kanta.

Legit.ng ta ruwaito Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a daren Laraba a shafinsa na Facebook, inda yace shuwagabannin biyu sun fara ganawa da juna ne tun daga karfe 9:30 har gaba da 10:30 na dare.

KU KARANTA: Babbar Kotu a Najeriya ta tsayar da ranar 3 ga watan Oktoba domin gurfanar da Allison Madueke

A ranar Laraba ne dai jama’an karamar hukumar Batsari suka dira fadar mai martaba sarkin Katsina, Abdulmuminu Kabir Usman dauke da gawarwakin mutane sama da goma da yan bindiga suka kashe a garin.

Da kyar da sudin goshi aka shawo kan fusatattun matasan a fadar Sarkin, inda daga bisani Sarkin da kansa ya fito yayi musu jawabi tare da tayasu jimami da alhinin rashin da aka yi, sa’annan ya jagoranci yi musu sallar jana’iza.

Kimanin kwanaki biyu da suka gabata ne wasu gungun yan bindiga suka halaka mutane 26 a wani hari da suka kai wasu kauyuka guda uku dake kananan hukumomin Dan Musa, Faskari da kuma Batsari.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun kashe mutane goma sha daya a kauyen Sabon Layin Galadima dake karamar hukumar Faskari, yayin da suka kashe mutane biyar a kauyen Mara Zamfarawa ta karamar hukumar Dan Musa, sai kuma mutane 18 a kauyen Yar Gamji dake Batsari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel