'Yan sanda sun kama ma'aikacin INEC da na'urorin tantance masu zabe

'Yan sanda sun kama ma'aikacin INEC da na'urorin tantance masu zabe

Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Akwa Ibom ta kama wani jami'in hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) bisa zargin sa da mallakar wasu na'urorin tantance masu zabe guda hudu ba bisa ka'ida ba.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Akwa Ibom, SP Odiko Macdon, ne ya tabbatar da hakan ga manemna labarai a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Ya ce rundunar ta saki ma'aikacin na INEC a kan beli yayin da take cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin.

A cewar Macdon, rundunar 'yan sanda ta rubuta wasikar neman karin bayani a kan na'urorin tantance masu zaben ga hukumar INEC.

"Tabbas jami'an mu sun kama wani ma'aikacin INEC da na'urorin tantance masu zabe har guda hudu. Bayan mun kama shi, mun aika wasika zuwa ga kwamishinan hukumar INEC na jiha domin neman karin bayani a kan dalilin samun na'urorin tare da ma'aikacin.

'Yan sanda sun kama ma'aikacin INEC da na'urorin tantance masu zabe

Na'urar tantance masu zabe
Source: Facebook

"Daga takaitaccen binciken da muka yi mun fahimci cewar yana aiki ne da sashen ICT na hukumar zabe, amma kwamishinan 'yan sanda ya umarci mu kara gudanar da bicike ta karkashin kasa a kan sa, musamman a kan dalilin da yasa na'urorin ke tare da shi.

"INEC ce kawai zata iya bayar da bayanin da zai gamsar a kan dalilin da yasa na'urorin ke hannun sa. Mu aiki mu shine kama masu laifi da kuma gurfanar da su," a cewar sa.

DUBA WANNAN: Zango na farko: Abinda yasa ban taba rushe ministoci ba - Buhari

Amma jam'iyyar APC reshen jihar Akwa Ibom tayi zargin cewar tun bayan kammala zabukan shekarar 2019, kwamishin INEC na jihar ke gudanar da canje-canje a kan na'urorin a sirrance domin boye magudin da ya hada baki da gwamnatin PDP wajen tafka wa.

Sai dai, jami'in hulda da jama'a na INEC a jihar, Mista Don Etukudo, a cikin jawabin da ya fitar ranar Laraba, ya ce jami'in ya yi amfani da na'urorin ne wajen bawa ma'aikatan wucin gadi horo lokacin zabukan 2019.

Kazalika ya bayyana cewar babu wasu bayanai a kan na'urorin da zasu iya canja sakamakon zabe ko kuma wani bayani da za a iya amfani da shi ko nema a kotun sauraron kararrakin zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel