Ta bayyana: Kamfanin jirgin kasar Misra da na Habasha na safarar muggan kwayoyi a Najeriya - Shugabar hukumar wajen Najeriya

Ta bayyana: Kamfanin jirgin kasar Misra da na Habasha na safarar muggan kwayoyi a Najeriya - Shugabar hukumar wajen Najeriya

Shugabar hukumar harkokin wajen Najeriya, Abike Dabiri-Erewa ta tuhumci kamfanin jirgin kasar Misra da na Habasha na laifin safarar muggan kwayoyi a filayen jirgin saman kasa da kasa dake Najeriya.

Dabiri-Erewa ta laburta hakan ne a ranar Laraba, 21 ga wata Mayu yayinda take jawabi gaban kwamitin majalisar dattawa kan abubuwan suka faru kan lamarin, Zainab Aliyu, da hukumar kasar Saudiyya ta damke da muggan kwayoyi.

Abike dabiri tace: "Muna da wasu kamfanonin jirgin wasu kasashe dake aiki a filayen jirginmu. Amma jirgin samam Misra da Habasha na safarar muggan kwayoyi a filayen jirginmu. Suna wannan abu ne tare da yan Najeriya."

Yayinda Shugaban kwamitin, Sanata Kabiru Gaya, ya bukaci bayanai kan na'urorin binciken jakunkuna a filayen jirgin saman, shugaban harkar tsaron hukumar jiragen saman Najeriya, Mista El-Yakub Usman Lamir, ya ce na'urar da ke filin saman Aminu Kano ba su da karfin gano muggan kwayoyi.

KU KARANTA: Hukumar Kwastam ta garkame mota jibge da Kodin na biliyoyin naira

Lamir ya kara da cewa jami'an binciken jakunkun 15 ke gudanar da bincike amma sai aka ragesu saboda korafe-korafen da matafiya ke yawan yi.

Waklin shugaban hukumar NDLEA, Mustapha Abdullah, ya bayyana cewa hukumar ba tada isassun karnukan gano muggan kwayoyi. Ya ce a fadin tarayya, karnuka 13 kadai ake da shi kuma duk suna Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel