Hukumar Kwastam ta garkame mota jibge da Kodin na biliyoyin naira

Hukumar Kwastam ta garkame mota jibge da Kodin na biliyoyin naira

Hukumar hana fsa kwabrin Najeriya wato Kwastam ta cika hannu da wata babbar mota cike da kwalaben maganin Kodin a jihar Legas.

Wannan abu ya kara nuna cewa ta'amuni da muggan kwayoyi babban kalubale ne duk da namijin aikin da hukumomin hana fasa kwabri na kwastam da hukumar yaki da muggan kwayoyi NDLEA ke yi.

Wannan babban lamu ya biyo bayan jibgin muggan kwayoyi da hukumar shiyar Zone A ta kama kimanin wata daya da ya gabata.

Kana hukumar ta damke motocin da aka kokarin shigo da su ta barauniyar hanya inda hukumar ta yi bayanin sabuwar hanyar da masu fasa kwabrin ke amfani da shi wajen shigo da sabbin motoci.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Jastis Zainab Bulkachuwa ta janye daga shari'ar zaben Buhari da Atiku

A cikin motar kuma, an samu busassun fatun jakuna, duk da cewar an haramta fita irin wadannan abubuwa.

A labari mai kama da haka, hukumar hana fasakauri ta Najeriya, ta sake da bujuro da kakar gwanjon hajoji domn sayar wa da mabukata cikin rahusa ta hanyar wani sabon shafi da ta kirkira a yanar gizo.

Hukumar Kwastam za ta yi gwanjon kayayyaki da ta kwace a hannun 'yan sumoga kama daga motoci na alfarma da kayayyaki daban daban musamman a rassan ta na jihohin Imo, Abia, Edo da kuma Delta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel