Zango na farko: Abinda yasa ban taba rushe ministoci ba - Buhari

Zango na farko: Abinda yasa ban taba rushe ministoci ba - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ya yanke shawarar kin canja ministocin sa a cikin shekaru uku da rabi da suka wuce, duk da matsin lambar da ya fuskanta, saboda irin gogewar da suke da ita da kuma nagartar su a bangaren iya shugabanci.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin taron mazalisar zartar wa ta tarayya (FEC) na karshe da aka yi a fadar shugaban kasa dake Abuja a ranar Laraba.

Ya bayyana cewar ministocin sun nuna juriya tare hada kai da juna wajen daukan matakan warware dumbin matsalolin da kasa ke fuskanta.

A cewar sa; "na san ba zaku taba manta cewar kasar mu na fuskantar dumbin matsaloli ba lokacin da muka karbi mulki.

Zango na farko: Abinda yasa ban taba rushe ministoci ba - Buhari

Buhari da ministoci yayin taron FEC
Source: Facebook

"Mun gaji nakasashen tattalin arziki wanda a sakamakon hakan muka shiga halin matsin tallin arziki a tsakiyar shekarar 2016. Ga kuma batun matsalar rashin tsaro da ta kara dagula al'amura.

"Wasu sun bayyana cewar ba zamu iya ba amma hakan bai saka kun karaya ba. Kun bani hadin kai wajen ganin mun sauke nauyin alkawuran yakin neman zaben da muka daukar wa 'yan Najeriya.

DUBA WANNAN: Buhari ya kara wa ministocin sa wa'adin ajiye aiki

"Wasu lokutan mu kan tafka mahawara yayin taron mu a kan yadda zamu gudanar da wani aiki ko daukan wani mataki domin cimma manufar gwamnatin mu. Hakan ya taimaka kwarai wajen yanke shawarwari masu ma'ana da nagarta.

"Wadan nan na daga cikin irin nagartar da na gani a tare da ku, kuma suka sa na rike ku har karshen zangon mulki na. Dukkanin ku kuna da baiwa ta musamman kuma kun bani muhimmiyar gudunmawa," a kalaman shugaba Buhari

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel