Ganduje ya nada kwamiti bayan manoma sun sulale da kudin Gwamnati

Ganduje ya nada kwamiti bayan manoma sun sulale da kudin Gwamnati

Mahmood Daneji wanda shi ne Darektan hukumar da ke kula da harkar noma da raya karkara a Kano ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta nada kwamitin da zai binciki bashin da aka ba manoma.

Farfesa Mahmood Daneji yake cewa wani kwamiti da aka nada na musamman zai yi kokarin bin diddikin Manoman da su ka karbi bashin babban bankin Najeriya na CBN domin su yi aikin gona.

Bankin dai ya bada kudi fiye da Naira miliyan 900 a tsarin da aka kawo na noman shinkafa, wanda aka samu Manoma 5, 540 da su ka amfana da kudin gwamnatin a jihar Kano inji Farfesa Daneji.

Sakataren gwamnatin Kano, Usman Alhaji, shi ne zai jagoranci wannan kwamiti da zai yi kokarin ganin ragowar kudin gwamnati da aka shigar wajen wannan aikin noma a shekarar 2016 sun fito.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta samu fiye da abin da ta sa rai daga hannun NNPC

Naira miliyan 50 ne kacal ya iya fiotowa daga cikin abin da aka rabawa wadannan manoma. Daneji ya nuna takaicinsa game da yadda Manoman su ka ki dawo da bashin kudin su na tunani sun ci bulus.

Shugaban kungiyar manoman jihar Kano, Alhaji Faruk Rabi’u yayi kira ga ‘ya ‘yan kungiyar ta su da su dawo da kudin da aka ba su aro. Har yanzu dai babu labari duk da wannan kira da aka yi.

Wannan ya sa gwamnatin Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ta kafa kwamiti da zai yi bincike domin bin inda wadannan Manoma su ke domin karbo wannan kudin noma da aka ba su aro tun tuni.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel