ASUU ta yi barazanar koma wa yajin aiki a kan rashin cika alkawarin gwamnati

ASUU ta yi barazanar koma wa yajin aiki a kan rashin cika alkawarin gwamnati

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU, ta yi barzanar tsunduma cikin wani sabon yajin aikin na sai baba-ta-gani a sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen rashin cika alkawali na yarjejeniyar da ta kulla a baya.

ASUU ta yi koken cewa kada a zargi mambobin a duk yayin da suka haifar da tsuguno ko kuma dakile gudanarwar harkokin karatu a jami'o'in kasar nan sakamakon yadda gwamnatin tarayya kawo wa yanzu ta gaza wajen cika alkawarin yarjejeniyar da ta kulla a bana.

Shugaban ASUU na kasa; Farfesa Biodun Ogunyemi

Shugaban ASUU na kasa; Farfesa Biodun Ogunyemi
Source: Getty Images

Farfesa Biodun Ogunyemi, shugaban kungiyar ASUU na kasa baki daya, shi ne ya yi wannan karin haske yayin ganawa da manema labarai na jaridar The Punch cikin birnin Abuja a ranar Larabar da ta gabata.

Ogunyemi ya yi tsokaci dangane da alkawalin da gwamnatin tarayya ta yiwa kungiyar ASUU na antaya ma ta Naira biliyan ashirin da biyar a bana kamar yadda Ministan ilimi na kasa Adamu Adamu ya bayar da tabbaci.

KARANTA KUMA: Hanyoyi 8 na kauce wa fadawa hannun masu garkuwa da mutane

Shugaban na ASUU ya ce kungiyar za ta ribaci N25bn wajen sallamar hakkokin malaman jami'o'i na alawus da rataya a wuyan gwamnatin tarayya da kawowa yanzu yarjejeniya da ta kulla 'yan watanni kadan da suka gabata lamarin ya zamto tamkar shuka ta ci shirwa.

Kungiyar ASUU ta janye yajin aikin ta na sai baba-ta gani a watan Fabrairun da ya gabata yayin da gwamnatin tarayya ta sha alwashin ba ta Naira biliyan ashirin da biyar cikin tsawon lokaci da ba zai wuce ranar 15 zuwa 28 ga watan Fabrairu na bana ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel