Abubuwa 17 da Buhari ya fada ma yan majalisarsa masu barin gado

Abubuwa 17 da Buhari ya fada ma yan majalisarsa masu barin gado

A jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a taron da ya saba gabatarwa kowanne sati da 'yan majalisar fadarsa, a wannan karon taron yau Laraba, 22 ga watan Mayu da suka gabatar shine taro na karshe da zai yi da ministocin nasa.

A taron shugaban kasar yayi bayani akan wasu muhimman abubuwa guda 17 ga ministocin nasa, ga bayanin da shugaban kasar yayi dalla-dalla:

1. Taron mu na yau shine taro na karshe da zanyi daku a wannan gwamnatin, kafin mu shiga sabuwar gwamnati a karo na biyu.

2. Zaman mu na farko a wannan majalisar mun yi shine a watan Nuwamba shekarar 2015. Sama da shekaru uku da suka shude, munyi ayyuka tare domin ganin mun cika alkawuran da muka dauka a lokacin yakin neman zabe. Ina da tabbacin cewa hadin kai da kuma ayyukan da muka yi tare ne ya kawo mu gaci.

3. Wasu daga cikin abokanan aikin mu da muka fara aiki tare da su, da yawa daga cikinsu basa nan.

4. Ina sake mika sakon ta'aziyya ta ga dan uwanmu kuma abokin aikin mu, marigayi James Ocholi SAN, wanda ya rasa ransa sanadiyyar hadarin mota shi da matarsa, Blessing da dansa Joshua, wanda suka rasu wata hudu bayan an rantsar dashi a matsayin minista.

5. Ina so mu saka shi da dukkanin iyalansa a addu'o'in mu.

6. Sannan ina mika sakon godiya ga wadanda suka yi murabus bamu samu damar kammala wannan gwamnati da su ba.

7. Idan ba ku manta ba lokacin da muka karbi gwamnatin nan, kasar nan na fuskantar kalubale kala daban-daban.

8. Mun tarar da kasar cikin matsanancin matsalar tattalin arziki. Hakan ya biyo bayan matsalar tsaro da ake fama da ita da kuma matsalar cin hanci da rashawa.

9. Na san da yawa daga cikinmu da tuni sun janye sun hakura, saboda da yawa daga cikin mutane na cewa halin da muka karbi kasar nan babu alamun zamu iya kawo wani canji ga al'umma. Amma kuma sai gashi mun hada karfi da karfe mun cika dukkanin alkawuran da muka dauka lokacin yakin neman zabe.

10. Jajircewar ku ce ta sanya tafiyar mu ta zo daya. Dukkanin ku kuna da kwarewa ta musamman. Kuma irin mu ne Najeriya take bukata a halin da take ciki yanzu.

11. Ina so kowannen ku ya san cewa yayi kokari gurin kawo cigaba ga kasar nan.

12. Kune mutanen da suka tsaya tsayin daka gurin ganin mun kwato kananan hukumomin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kwace.

13. Kune kuka jajirce wurin ganin an kaddamar da hanyoyi a kasar nan, kuma kune kuka yi sanadiyyar samar da titin jirgin kasa, da kuma gyara filayen jiragen saman mu.

14. Ina so na sanya ku a tarihin kasar nan na irin ayyukan da kuka zage kuka yi a cikin shekaru uku da suka gabata.

KU KARANTA KUMA: An roki Buhari ya ajiye Lai Mohammed a karo na biyu

15. Duk da cewa wannan shine taron mu na karshe a wannan gwamnatin, amma duk da haka ina so ku cigaba da aiki har ranar Talata 28 ga watan Mayu, 2019, daga nan ina so ku danka ragamar ayyukan ga sakatarorin ku.

16. A karshe ina yi muku godiya kwarai da gaske da har kuka amince kuka bautawa kasar ku, a wannan matsanancin halin da take ciki.

17. Ina yi muku fatan alkhairi, kuma ina yi muku fatan cigaba a rayuwar ku data iyalan ku dama kasa baki daya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel