Jerin jihohi 14 da basu karbi kason kudin tallafin kiwon lafiya ba

Jerin jihohi 14 da basu karbi kason kudin tallafin kiwon lafiya ba

Rahotanni sun nuna cewa har yanzu akwai akalla jihohin kasar 14 da basu amshi kudin tallafin kiwon lafiya na ‘Basic Health Care Provision Fund (BHCPF)’ ba.

Ministan lafiya, Farfesa Isaac Adewole ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 21 ga watan Mayu.

Ministan ya bayyana hakan ne a majalisar dattawa inda ya kara da cewa jihohi 22 ne suke karban wannan tallafi.

Ya ce rashin nuna ra’ayin karban tallafin da rashin cika sharudan samun tallafin na daga cikin dalilan da ya hana wadannan jihohin samun karban kason su.

Jerin jihohi 14 da basu karbi kason kudin tallafin kiwon lafiya ba

Jerin jihohi 14 da basu karbi kason kudin tallafin kiwon lafiya ba
Source: Facebook

“Sharudan samun tallafin sun hada da kafa hukumar kula da aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko, Kafa inshoran kiwon lafiya na jihar da bada gudunmawar Naira biliyan 100,” cewar shi

KU KARANTA KUMA: Majalisar dokoki jihar Zamfara ta kirkiri sabuwar masarauta

Ga jerin jihohin das u karban wannan tallafi kamar haka:

1. Jihar Kebbi

2. Jihar Jigawa

3. Jihar Akwa Ibom

4. Jihar Cross River

5. Jihar Gombe

6. Jihar Rivers

7. Jihar Borno

8. Jihar Zamfara.

9. Jihar Ondo

10. Jihar Benue

11. Jihar Taraba

12. Jihar Nasarawa

13. Jihar Ogun

14. Jihar Sokoto.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel