Tiriliyan 1.2 mu ka zuba a asusun Gwamnatin Najeriya bara – NNPC

Tiriliyan 1.2 mu ka zuba a asusun Gwamnatin Najeriya bara – NNPC

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC ya bayyana cewa ya sauke duk nauyin gwamnatin Najeriya da ke kan sa a shekarar da ta gabata bayan kamfanin ya zuba makudan kudi a asusun Najeriya.

Kamar yadda mu ka samu labari, wani babban Darekta na kamfanin na NNPC ya bayyana cewa sun ba gwamnatin Najeriya Naira tiriliyan 1.26 a shekarar da ta gabata. Wannan kudi ya wuce abin da gwamnatin kasar ta sa ran samu.

Mista Godwin Okonkwo yake cewa gwamnati ta sa ran cewa za ta samu tiriliyan 1.22 ne daga hannun kamfanin. A karshen shekara dai abin da NNPC ta zuba a cikin asusun gwamnatin Najeriya ya haura hakan inda ya kai tiriliyan 1.6

KU KARANTA: Kamfanin NNPC ya bayyana inda aka kwana a shirin daukar aiki

Tiriliyan 1.2 mu ka zuba a asusun Gwamnatin Najeriya bara – NNPC

Najeriya ta samu sama da Tiriliyan 1 daga hannun NNPC a 2018
Source: Depositphotos

Godwin Okonkwo, wanda yana cikin manyan jami’an NNPC yake cewa gwamnati ta samu rarar Naira biliyan 41 daga hannun su. Okonkwo ya bayyana wannan ne a lokacin da ya wakilci shugaban kamfanin man watau Kanti Baru a majalisa.

Darektan ya wakilci Maikanti Baru ne a gaban ‘yan majalisar tarayya yayin da ake sauraron ta-bakin su wajen wani binciken ma’aikatu da ake yi a game da rashin zuba kudin da su ka tatso zuwa cikin asusun gwamnatin tarayyar kasar.

A bara an yi kasafin cewa za a rika saida ganga miliyan 2.3 a duk rana. Sai dai abin da aka rika samu bai haura ganga miliyan 1.9 ba. Kamfanin ya kuma bayyana cewa ya kusa fitar da rahoton binciken akawun din su da aka yi a 2018.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel