An roki Buhari ya ajiye Lai Mohammed a karo na biyu

An roki Buhari ya ajiye Lai Mohammed a karo na biyu

Kungiyar dattawan yankin Kwara ta Kudu na jam'iyyar All Progressive Congress (APC) sun nuna rashin goyon bayan su ga nadin Alhaji Lai Mohammed a matsayin ministan sadarwa da al'addu.

Kungiyar ta bukaci a sake zabo wani mutum daga yankin Kwara ta Kudu domin maye gurbin ministan mai ci yanzu wanda suka ce bai tabuka wani abin azo a gani ba kuma a matsayinsa na dan jihar Kwara.

Dattawan sun ce duk wanda za a nada daga yankin ya zama goggage a siyasar cikin gida kuma ya kasance mai kaunar jama'a da kuma son cigaban jihar Kwara.

An roki Buhari ya ajiye Lai Mohammed a karo na biyu

An roki Buhari ya ajiye Lai Mohammed a karo na biyu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Tsaffin hadiman minista sun maka shi a kotu saboda kin biyansu albashi

Kungiyar ta bayar da wannan sanarwan ne cikin wani sako mai dauke da sa hannun shugaban ta, Cif J.B Ayeni da sakataren ta, Injiniya Jide Usman da aka fitar bayan wani taron gaggawa da sukayi a gidan Cif Ayeni a Ilorin.

Kungiyar da nesanta kanta daga wani sakon bayan taro da Kungiyar APC na karamar hukumar Irepdun, karkashin jagorancin Dr Hezekiah Oyedapo ta fitar na goyon bayan ministan.

"Kwara ta Kudu ta kunshi kananan hukumomi guda bakwai wanda hakan ke nuna ta fi karamar hukumar Irepdun girma wadda duka ba ta fi 10% na yankin ba. Kananan hukumomin sun hada da Ifelodun, Oyun, Offa, Isin, Oke-ero, Ekiti and Irepodun," inji sanarwar.

Kungiyar ta kuma karyatta ikirarin da akayi na cewa Lai Mohammed ne sanadiyar nasarar da jam'iyyar APC ta samu a jihar Kwara yayin babban zaben shekarar 2019.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel