Yanzu-yanzu: Jastis Zainab Bulkachuwa ta janye daga shari'ar zaben Buhari da Atiku

Yanzu-yanzu: Jastis Zainab Bulkachuwa ta janye daga shari'ar zaben Buhari da Atiku

Shugaban kotun daukaka karan Najeriya, Jastis Zainab Bulkachuwa, ya janye daga shari'ar kotun zaben da ke tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da abokin hamayyarsa, Alhaji Atiku Abubakar a ranar Laraba, 21 ga wtaan Mayu, 2019 a birnin tarayya Abuja.

Hakan ya biyo bayan doguwar zaman da akayi yau a kotun zaben kan bukatar da jam'iyyar PDP ta gabatar akan Jastis Bulkachuwa.

Jam'iyyar People's democratic party PDP ta bukaci Zainab Bulkachuwa ta janye daga karar saboda uwargice ga zababben sanata karkashin jam'iyyar All Progressives Congress.

Lauyan Atiku Abubakar, Livy Ozuokwu, ya mika wannan bukata ne saboda suna tsoron cewa Zainab Bulkachuwa za ta iya rashin gaskiya a karar.

Ku saurari cikakken rahoton....

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel