Matsin tattalin arziki: Najeriya kan iya koma wa ruwa tsundum - CBN

Matsin tattalin arziki: Najeriya kan iya koma wa ruwa tsundum - CBN

Gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana tsoron sa a kan yiwuwar Najeriya ta kara koma wa cikin matsin tattalin arziki matukar ba a dauki matakan shawo kan matsalar rashin aikin yi da wasu rigingimu dake damun tattalin arziki ba.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewar Emefiele ya bayyana hakan ne yayin gabatar da lakca a wurin bikin yaye dalibai a jami'ar Benin, wanda aka yi a ranar Laraba, 22 ga watan Mayu.

A cewar sa, dole hukumomi su fara tunani domin bullo da tsare-tsaren da zasu kawo karshen kalubalen da tattalin arzikin kasa ke fuskanta.

"Za ku fahimci cewar a cikin lakca ta na nuna shakku a kan rashin tabbas ta fuskar tattalin arziki, tattalin arzikin duniya na fuskantar kalubalen da ko muna so ko bama so, zai iya haifar da matsin tattalin arziki.

Matsin tattalin arziki: Najeriya kan iya koma wa ruwa tsundum - CBN

Gwamnan CBN; Godwin Emefiele
Source: Depositphotos

"Abin tambaya a nan shine, me muke yi a Najeriya, musamman shugabannin mu, wajen ganin shirya domin fuskantar wani matsin tattalin arzikin da kan iya faruwa?"

"Mun yi sa'a mun fita daga cikin halin matsin tattalin arziki. Mun ga yadda matsin tattalin arziki ya ragu daga kaso 18.72% a shekarar 2017 zuwa 11.37% a yau.

DUBA WANNAN: Buhari ya kara wa ministocin sa wa'adin ajiye aiki

"Asusun gwamnati ya samu habaka, kasuwar canjin kudi ta samu daidaito amma duk da haka akwai 'yan matsaloli, wacce babbar su ita ce matsalar rashin aiki a tsakanin 'yan kasa," a cewar Emefiele.

Kazalika ya bayar da tabbacin cewar babban bankin kasa zai cigaba da daukan matakan da zasu rage radadin matsin tattalin arziki, musamman wadanda kan iya samun tushe daga kasashen ketare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel