Direba ya kashe yara hudu, ya jikkata sama da goma a jihar Anambra

Direba ya kashe yara hudu, ya jikkata sama da goma a jihar Anambra

- Wani direban mota ya kashe daliban makarantar firamare guda hudu ya kuma jikkada sama da guda goma sanadiyyar gudun da yake yi wanda ya wuce kima

- Rahotanni sun nuna cewa motar ta kwace daga hannun direban ne sanadiyyar birki da ya shanye a lokacin da ya kawo kusa da daliban

Wasu daliban makarantar firamare guda hudu sun gamu da ajalinsu, sakamakon wani direban mota da ya bi ta kansu akan tsohuwar hanyar Oba zuwa Nnewi dake garin Ugwube cikin karamar hukumar Idemili, jihar Anambra.

Daliban an bayyana cewa suna kan hanyarsu ta zuwa gida yayin da suka tashi daga makaranta, lokacin da motar ta kwace daga hannun direban ta yi kansu.

Mun samu rahoton cewa yara hudu ne suka rasa rayukansu a take a gurin, yayin da sama da yara goma kuma suka ji munanan raunuka.

Direba ya kashe yara hudu, ya jikkata sama da goma a jihar Anambra

Direba ya kashe yara hudu, ya jikkata sama da goma a jihar Anambra
Source: Facebook

Wani wanda lamarin ya faru akan idonsa ya bayyana cewa motar ta taho daga garin Onitsha ne, yayin da yake gudun da ya wuce kima, sai birkin motar ya shanye, hakan yayi sanadiyyar bi ta kan daliban.

Ya ce: "Daliban sun fito da yawansu a lokacin da aka tashe su daga makarantar da misalin karfe 2 na rana.

KU KARANTA: Jihohi da yawa za su talauce idan aka fara biyan sabon albashi - Tsohon Kwamishinan Kudi

"Suna tafiya akan tsohuwar hanyar Oba zuwa Nnewi yayin da direban motar kirar Infinity Jeep mai lambar MYB 22 AAA, ta bi ta kan daliban, inda ta kashe guda hudu ta raunata da yawa daga cikinsu."

A bayyana cewa an kai daliban da suka samu raunukan asibiti mafi kusa domin karbar magani.

Sannan mun samu rahoton cewa biyu daga cikin daliban da suka rasa rayukansu, 'yan gida daya ne.

Haka kuma shugaban ofishin 'yan sandan Oba, Mr. Ifeanyi Abanaofor, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel