Babu abinda gwamnoni zasu iya akan matsalar tsaro, inji Ishaku

Babu abinda gwamnoni zasu iya akan matsalar tsaro, inji Ishaku

-Gwamna jihar Taraba ya nuna damuwarsa akan tabarbarewar tsaro a yankin arewacin Najeriya, duba ga cewa gwamnoni basu da ikon kawo karshe wannan lamari.

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku a ranar Laraba ya koka akan bukatar kafa yan sanda jihohi domin rage matsalolin tsaro a kasar nan.

Ishaku yayi wannan kiran ne yayin da yake amsa tambayoyin yan jarida a Jalingo jim kadan bayan ya kammala kaddamar da ta tallafi na musamman ga manoman jihar Taraba inda aka raba masu takin zamani, maganin kwari da kuma irin suka.

Babu abinda gwamnoni zasu iya akan matsalar tsaro, inji Ishaku

Babu abinda gwamnoni zasu iya akan matsalar tsaro, inji Ishaku
Source: Twitter

KU KARANTA:Rashin tsaro: Shehu Sani yayi magana mai zafi akan harin da ya kashe mutum 30 a Katsina

Gwamnan yace a matsayinshi na gwamna babu abinda zai iya yi akan matsalar tsaro, daga bisani kuma ya yi kira ga al’ummar jihar da su cigaba da rokon Allah ya kawo masu saukin lamarin ta yadda jiharsu zata zauna lafiya.

“ Idan wani gwamna yace daku zai iya kawo karshe wannan rashin tsaro to hakika karya yake. A matsayinmu na gwamnoni bamu da ikon akan yan sanda ko sojoji, a don haka bamu iya magance matsalar da ta shafi rashin tsaro.

“Mun dade muna neman a kafa hukumar yan sanda ta jihohi amma babu wanda ya biyamu akan wannan batu. Kundin tsarin mulkin kasarmu ba sanya ikon kula da tsaron kasa a hannun gwamnonin jihohi ba. A don haka ni a karan kaina ina addu’ar ganin karshe wannan al’amari kuma na nemi jama’ar gari su cigaba da yin addu’ar samun zaman lafiya.” A cewar Darius Ishaku.

A cikin kudurinsa na shekaru hudu da ke tafe wanda zai kasance wa’adinsa na biyu a kan mulki, gwamnan ya bayyana cewa zai mayar da hankali akan ayyukan da ya riga ya fara musamman fannin habbaka tattalin arziki da kuma noma a jihar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel