Cikin Hotuna: Mataimakin shugaban kasa ya gana da masu sanya hannun jari a shirin habaka tattalin arziki na gwamnatin tarayya, NZESCO

Cikin Hotuna: Mataimakin shugaban kasa ya gana da masu sanya hannun jari a shirin habaka tattalin arziki na gwamnatin tarayya, NZESCO

Cikin fadar shugaban kasa ta Villa dake garin Abuja, mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Laraba, 22, ga watan Mayun 2019, ya gana da tawagar masu sanya hannun jari a shirin nan na habaka tattalin arziki na gwamnatin tarayya, NZESCO.

Mataimakin shugaban kasa tare da Ministan shari'a kuma lauyan kolu na kasa, Abubakar Malami da kuma Ministan Masana'antu da sanya hannun jari na kasa, Okechukwu Enelemah, sun karbi bakuncin manyan bakin a fadar shugaban kasa.

Manyan bakin masu taka rawarar ganin a shirin nan na habaka tattalin arziki na gwamnatin tarayya sun hadar da Olukayode Peter, Injiniya Battah Ndirpaya, Leonard Kange, da kuma Gbenga Oyebode.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta kaddamar da shirin NZESCO, Nigeria Special Economic Zones Company, domin zage dantsen a fagen bunkasa tattalin arziki ta hanyar masana'antu da babbar manufa ta inganta ci gaban kasar nan.

Osinbajo yayin karbar bakuncin masu sanya hannun jari a shirin NZESCO

Osinbajo yayin karbar bakuncin masu sanya hannun jari a shirin NZESCO
Source: Facebook

Osinbajo tare da Ministocin Buhari bayan karbar bakuncin masu sanya hannun jari a shirin NZESCO

KARANTA KUMA: Jerin ministocin Buhari, sunaye, ma'aikatu da kuma jihohin su

Osinbajo tare da Ministocin Buhari bayan karbar bakuncin masu sanya hannun jari a shirin NZESCO

Osinbajo tare da Ministocin Buhari bayan karbar bakuncin masu sanya hannun jari a shirin NZESCO
Source: Facebook

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel