Ku zauna a gida ko ku dandana kudar ku, hukamar ‘yan sanda ta gargadi kungiyar IPOB

Ku zauna a gida ko ku dandana kudar ku, hukamar ‘yan sanda ta gargadi kungiyar IPOB

-Hukumar yan sanda a jihar Anambra ta gargadi IPOB akan shirin da take yi na ranar 30 ga watan Mayu.

-Idan kuna neman kanku da lafiya to ku zauna a gida, furucin da hukumar yan sandan tayi amfani da shi kenan domin gargadi ga kungiyar.

Hukumar yan sandan jihar Anambra ta gargadi yan kungiyar tawaye ta Baifra da su kasance a cikin gidajensu in dai har suna nemawa kawunansu zaman lafiya.

Wannan gargadin daga hukumar ‘yan sanda ya biyo bayan wata sanarwa da kungiyar tawayen da bada a kwanakin baya cewa, ranar 30 ga watan Mayu zasu tsayar da duk wata hada-hada a yankin kudu maso gabashin kasar nan domin tunawa da yan uwansu da aka kashe a irin wannan rana.

Ku zauna a gida ko ku dandana kudar ku, hukamar ‘yan sanda ta gargadi kungiyar IPOB

Ku zauna a gida ko ku dandana kudar ku, hukamar ‘yan sanda ta gargadi kungiyar IPOB
Source: UGC

KU KARANTA:Azumin Ramadana: Gwamnatin jihar Sakkwato ta bude cibiyoyi 138 domin bude baki

Kungiyar tawayen tayi alwashin yin amfani da wannan ranar domin juyayi da kuma tunawa da yan uwansu da aka kashe a yakin basasan da ya auku tsakanin shekarar 1967 zuwa 1960, wadanda jami’an tsaron Najeriya suka kashe a sassa daban daban dake fadin kasar nan.

A wani zance da ya fito daga wurin jami’in hulda da jama’a na yan sandan jihar Anambra, Haruna Muhammad gargadi yayi gay an kungiyar ta IPOB na cewa kada su sake su fara yin wannan abu da suke shirin yi saboda kungiyar tasu ma haramtacciyar kungiyace.

Daga cikin abinda zancen ya kunsa, akwai gargadi tare da jan kunne ga kungiyar IPOB na cewa kada su fito ranar 30 ga wata idan ba haka ba zasu hadu da fushin jami’an yan sanda.

Har wa yau a ciki zance, hukumar yan sandan jihar ta nemi jama’ar garin da suyi watsi da duk wani kira da kungiyar keyi a garesu cewa ranar 30 ga watan Mayu babu fita wurin sana’a. Akwai tanadin tsaron na musamman a wannan rana saboda haka kowa ya fita zuwa wurin nema halaliyarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel