Da duminsa: Buhari ya kara wa ministocin sa wa'adin yin murabus

Da duminsa: Buhari ya kara wa ministocin sa wa'adin yin murabus

A yayin da ake saka ran cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rushe ministocinsa a ranar Laraba, 22 ga watan Mayu, yayin zaman majalisar zartawar na tarayya (FEC) na karshe a zangon sa na farko, shugaban kasar ya shaida musu cewar su cigaba da aiki har zuwa ranar 28 ga watan Mayu.

Buhari ya umarci ministocin su cigaba da zama ofis domin gudanar da aiyukan su har zuwa ranar Talata, 28 ga watan Mayu.

Shugaba Buhari ya bayyana musu cewar wannan shine zama na karshe da FEC tayi a zangon mulkin sa na farko da ya fara daga shekarar 2015, amma ya fada wa ministocin su cigaba da aiki tare da shirin mika aiki ga manyan sakatarorin ma'aikatun su.

Ya fada wa ministocin su mika takardun barin aikin su ga manyan sakatarorin a ranar ta Talata, 28 ga watan Mayu, jajiberin ranar da za a sake rantsar da shi a matsayin zababben shugaban kasa a karo na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel