Gwamna Yari ya yi watsi da jama'arsa ya tare a Abuja - Wani sanata ya yi korafi

Gwamna Yari ya yi watsi da jama'arsa ya tare a Abuja - Wani sanata ya yi korafi

Wani sanatan Najeriya, Victor Ameh daga jihar Anambra ya zargi gwamnan Jihar Zamfara, Gwamna Abdulaziz Yari da watsi da al'ummar jiharsa a lokacin da ake fama da kallubalen tsaro.

Mr Umeh dan jam'iyyar APGA ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan kashe-kashen da akeyi a Jihar Rivers inda ya ce gwamnan ya tsere daga Arewa maso Yamma ya koma Abuja da zama saboda rashin tsaro.

Dan majalisar yana magana ne a kan kudirin da Andrew Uchendu (Rivers PDP) ya gabatar a kan kashe-kashen da akeyi a Jihar Rivers.

Ya bayar da misalin abinda ya faru a ranar 19 ga watan Mayu a garin Isiodu a karamar hukumar Emoha inda wasu 'yan bindiga suka kai farmaki garin suka kashe mutane uku suka kone gawarwakinsu.

DUBA WANNAN: Rudani: Kwamandan soji ya kaiwa tawagar mataimakin gwamna hari a Maiduguri

Tsaro: Yari ya yi watsi da jama'arsa ya tare a Abuja - Wani sanata ya yi korafi

Tsaro: Yari ya yi watsi da jama'arsa ya tare a Abuja - Wani sanata ya yi korafi
Source: Twitter

Ya yi korafin cewa ba a dauki wata mataki kwakwara ba hakan yasa kashe mutane ya zama ruwan dare a jihar Rivers.

A yayin da ya ke tofa albarkacin bakinsa, Mr Umeh ya ce gwamnonin Najeriya ba su tabuka abinda ya dace suyi a kan batun tsaro a kasar nan.

"Ana ta cigaba da kashe-kashe a wasu jihohi inda gwamnoninsu ba su daukan matakai. Kashe-kashen da akeyi a Rivers ya kazanta. Ya kamata gwamnan jihar Rivers ya kawo karshen kashe-kashen nan. Gwamnonin za su iya tsayar da kashe-kashen idan sun dauki matakan da suka dace.

"Ya dace gwamnoni su taimaka wurin magance wannan matsalar. Ba maganan 'yan sanda bane kawai. Ya kamata gwamnoni su sanya kudi a harkar samar da tsaro. Gwamnoni suyi amfani da kudaden tsaro da ake basu, dama shine amfanin kudin.

"Idan ku ka biya kudi domin a gudanar da bincike, cikin kwanaki uku za a gano wadanda ke aikata kashe-kashen saboda mutanen da ke zaune kusa da makasan sun san su."

Dan majalisan ya ambaci Gwamna Yari na jihar Zamfara inda ya ce, "Wasu gwamnoni sun tsere daga jihohinsu, sun koma Abuja da zama. Idan kayi tambaya za ka ji ana cewa an kashe-kashe da yawa kamar a jihar Zamfara.

"Yanzu ya dawo Abuja da zama yana hallartan taruruka yayin da aka kashe jama'a a jiharsa a kowanne rana."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel