Zabe: Dan takarar jam'iyyar GPN ya janye karar da ya shigar da Ganduje

Zabe: Dan takarar jam'iyyar GPN ya janye karar da ya shigar da Ganduje

Dan takarar gwamna na jam'iyyar Green Party of Nigeria (GPN), Abdulkarim Abdussalam ya janye karar da ya shigar na kallubalantar nasarar Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano.

A cikin takardar janye karar da ya shigar ta hannun lauyansa, Ibrahim Sa'ad, Abdussalam ya ce ya janye karar ne saboda a samu zaman lafiya a jihar.

Ya ambaci sashi na 1 (a) da (b) na dokar zabe wurin janye kararsa.

Shugaban kotun sauraron kararrakin zabe, Jastis Halima Mohammed ta amince da bukatar lauyan Abdussalam kuma tayi watsi da karar.

Zabe: Dan takarar jam'iyyar GPN ya janye karar da ya shigar da Ganduje

Zabe: Dan takarar jam'iyyar GPN ya janye karar da ya shigar da Ganduje
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kannywood: Ban durkusa domin bawa Nabruska hakuri ba - Hadiza Gabon

A halin yanzu, karar da ke gaban kotun kawai itace wadda dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, Abba Kabir-Yusuf ya shigar na kallubalantar nasarar Ganduje bayan an gudanar da zaben kece raini.

Kazalika, A ranar Laraba kotun ta gargadi 'yan jarida masu sauya yadda shari'ar ke gudana a yayin wallafa rahotanin su.

Shugaban kotun, Mrs Muhammad ta bayar da gargadin ne a zaman farko da aka gudanar a harabar kotun da ke Miller Road a jihar Kano.

"Muna sa ran samun sahihan rahoto daga 'yan jarida domin duk wani rahoton karya da ka iya tayar da zaune tsaye rashin girmama kotu ne," inji Mrs Muhammad.

Ta ce kotun za ta bawa dukkan jam'iyyun siyasa damar gabatar da hujjojinsu a gabanta tare da yiwa kowa adalci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel