Babbar Kotu a Najeriya ta tsayar da ranar 3 ga watan Oktoba domin gurfanar da Allison Madueke

Babbar Kotu a Najeriya ta tsayar da ranar 3 ga watan Oktoba domin gurfanar da Allison Madueke

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Apo na babban birnin tarayya Abuja, ta sanar da ranar 3 ga watan Oktoba a matsayin ranar da take bukatar ganin an gurfanar da tsohuwar ministar man fetir a gwamnatin Goodluck Jonathan, Diezani Allison Madueke.

Tun a ranar 25 ga watan Feburairu ne kotun ta baiwa hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC damar kamo Diezani, da shugaban kamfanin man fetir na Atlantic Engery Drilling, Jide Omokore akan tuhume tuhume guda 5 da suka danganci rashawa.

KU KARANTA: Kira ga barayin gwamnati su tuba, su mayar da kudaden da suka sata albarkacin watan Ramadan

Babbar Kotu a Najeriya ta tsayar da ranar 3 ga watan Oktoba domin gurfanar da Allison Madueke

Babbar Kotu a Najeriya ta tsayar da ranar 3 ga watan Oktoba domin gurfanar da Allison Madueke
Source: UGC

Daga bisani lauyan EFCC Faruk Abdullahi ya shaida ma kotun cewa basu samu gurfanar da wadanda ake tuhumar ba sakamakon basa kasar, amma yace sun mika takardar bukatar kamota ga babban lauyan gwamnati, daga kasar Birtaniya inda take buya.

Amma ya danganta rashin gurfanar Mista Omokore gaban kotun ga gazawar hukumar EFCC ta wajen mika masa sammacin kotun, da wannan ne lauya Faruk ya nemi kotu ta dage sauraron karar har sai sun mika masa takardar sammacin kotu.

Shima a nasa bangaren, lauyan Omokore, Adeniyu Adebgonmire ya bayyana ma kotu cewa a shirye wanda yake karewa yake ya gurfana gabanta, amma ba zai gurfana ba har sai an bi hanyoyin sanar dashi sammacin kotun kamar yadda doka ta tanada.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu ne sai Alkalin Kotun ya sanya ranar 3 ga watan Oktoba don baiwa EFCC damar gurfanar da dukkanin mutanen biyu da hukuma take tuhuma, daga nan kuma a fara sauraron karar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel