Buhari ya nada Dadi-Mamud a matsayin sabon darektan hukumar NIS

Buhari ya nada Dadi-Mamud a matsayin sabon darektan hukumar NIS

Shuagaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dakta John Dadi-Mamud a matsayin sabon darektan cibiyar koyar da wasanni ta kasa (NIS).

Takardar nadin da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta bayyana cewar an nada Dadi-Mamud, tsohon mataimakin darekta a NIS, ya jagoranci cibiyar na tsawon zango guda mai wa'adin shekaru hudu.

Dadi-Mamud, mai shekaru 53 a duniya, ya fito ne daga jihar Kogi kuma ya yi karatu a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Yana da digiri na biyu da na uku a bangaren ilimin kimiyyar wasanni da motsa jiki.

A jawabin Nneka Ikem-Anibeze, mai taimaka wa ministan wasanni, Solomon Dalung, a bangaren kafafen yada labarai, ta ce Dadi-Mamud ya rike mukamai da dama a cibiyar NIS.

Buhari ya nada Dadi-Mamud a matsayin sabon darektan hukumar NIS

Buhari
Source: Facebook

Ya taba kasancewa mukaddashin darektan NIS da kuma shugabantar harkokin koyarwa a cibiyar.

DUBA WANNAN: An sako jami'an hukumar kiyaye hadura da aka yi garkuwa da su

Ya taba rike mukamin shugaban sashen bincike a NIS, ya kuma taba zama sakatare a kungiyar masu kurme (swimming) reshen Lokoja. Ya taba koyarwa a makarantar horon malaman koyon harshen larabci (Arabic) dake Kano.

Sabon nadin ya fara aiki ne daga ranar 14 ga watan Mayu, kuma ya karbi aiki ne daga hannun tsohon shugaban NIS, Dakta Chukwudi Eke, da wa'adin mulkinsa ya kare a ranar Litinin, 10 ga watan Mayu.

Aikin cibiyar NIS shine bincike da koyar da wasanni a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel