An sako jami'an FRSC da aka yi garkuwa da su

An sako jami'an FRSC da aka yi garkuwa da su

An sako jami'an hukumar kiyaye hadura ta tarayya (FRSC) biyu da masu garkuwa da mutane suka sace ranar Litinin.

Kakakin hukumar na kasa, Bisi Kazeem, ya tabbatar wa da jaridar Premium Times labarin sakin jami'an ranar Laraba.

Wasu 'yan bindiga ne suka sace ma'aikatan biyu; Abioye da Bayegunmi, a Iwajara dake karamar hukumar Oriade a jihar Osun.

Da sanyin safiyar ranar Talata ne masu garkuwa da jami'an suka nemi a biya su miliyan N1 kudin fansa kafin su sake su.

An sako jami'an FRSC da aka yi garkuwa da su

Jami'an FRSC
Source: Depositphotos

An sako jami'an ne ranar Talata da daddare.

Babu tabbacin cewar ko an biya masu garkuwar kudin da suka nema kafin su saki jami'an.

Da aka tuntubi Kazeem ta hanyar takaitaccen sakon wayar hannu a kan labarin sakin jami'an, sai ya amsa sakon da cewar; "an sako su."

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun harbe Shaho; shugaban gungun masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja

Ya kara da cewa hukumar FRSC zata fitar da karin bayani zuwa anjima.

Batun satar mutane tare da yin garkuwa da su har sai an biya kudin fansa ya zama ruwan dare a sassan Najeriya duk da irin kokarin da hukumomin tsaro ke yi wajen dakile wannan muguwar sana'a. Jami'an tsaro sun kama dumbin masu garkuwa da mutane a sassan kasar nan a 'yan kwanakin baya bayan nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel