Kira ga barayin gwamnati su tuba, su mayar da kudaden da suka sata albarkacin watan Ramadan

Kira ga barayin gwamnati su tuba, su mayar da kudaden da suka sata albarkacin watan Ramadan

Kungiyar kare hakkin Musulmai, MURIC, tayi kira ga yan Najeriyan da suka san sun wawuri kudin gwamnati ko kuma suka yi wadaka da kashe mu raba da arzikin jama’a dasu yi gaggawar tuba ga Allah tare da mayar da abinda suka sata albarkacin watan Ramadan.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana haka a ranar Talata, 21 ga watan Mayu inda yace sahihin hanyar neman gafara ga barayin gwamnati shine su fara tuba, su mayar da kudi ko kayan da suka sata, sa’annan su kudurci aniyar ba zasu sake sata ba.

KU KARANTA: EFCC ta titsiye jami’an gwamnatin Kwara akan bahallatsar N400m

Kira ga barayin gwamnati su tuba, su mayar da kudaden da suka sata albarkacin watan Ramadan

Akintola
Source: UGC

“Mun kira ga barayin gwamnati dasu gaggauta tuba a cikin watan Ramadan sakamakon watane da Allah Ke gafarta ma bayinsa, shi yasa muke kira a gareku daku tuba, ku mayar da abinda kuka dauka sa’annan kada ku kara yi a gaba.

“Allah baya son rashawa, saboda rashawa mugun abu ne da idan al’umma bata kawar dashi ba zai kawar da ita, rashawa na kara nisan bambamci tsakanin Talaka da attajiri ne, yayin da Musulunci ke rage wannan tazara dake tsakanin masu kudi da talakawa.

“Shi yasa Allah Ya haramta karbar cin hanci da rashawa a cikin Al-Qur’ani, Surah ta 2 aya ta 188, da kuma Surah ta 4 Aya ta 29-30, bugu da kari Allah Ya haramta tara arzikin da ya wuce misali a cikin sura ta 102 Aya ta 1-8 da kuma Surah ta 104 Aya ta 1-9.” Inji shi.

Haka zalika Malamin addinin Islaman ya kawo Hadisan Annabi Muhammadu Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi dayake nuna haramcin karbar rashawa da cin hanci, inda yace duk mai karbar rashawa baya tare dashi, haka zalika duk mai karbar rashawa ba zai shiga Aljanna ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel