Azumin Ramadana: Gwamnatin jihar Sakkwato ta bude cibiyoyi 138 domin bude baki

Azumin Ramadana: Gwamnatin jihar Sakkwato ta bude cibiyoyi 138 domin bude baki

-Gwamnatin ta fitar da kudin da yawansu ya kai N380m domin yin wannan aiki na neman lada a fadin babban birnin jihar.

-Akwai kimanin kungigoyi 231 wadanda ke amfana daga cikin taimakon wannan kwamitin dake kula da ciyarwar.

Shugaban kwamitin ciyar da abinci na watan Ramadana Mallam Lawal Maidoki shi ne ya fadi wannan sanarwa cewa an bude cibiyoyin bude baki a birnin Sakkwato guda 138 domin azumin bana.

Ya kuma kara da cewa, kimanin kungiyoyi 231 ne suka samu taimako daga wajen su domin cigaba da gudanar da wannan ciyarwa har zuwa karshen watan Ramadana.

Azumin Ramadana: Gwamnatin jihar Sakkwato ta bude cibiyoyi 138 domin yin bude baki

Azumin Ramadana: Gwamnatin jihar Sakkwato ta bude cibiyoyi 138 domin yin bude baki
Source: UGC

KU KARANTA:Ta leko ta koma: Hukumar INEC ta karbe takardar shaidar lashe zabe daga hannun yan majalisa biyu a Kaduna

Maidoki yayi wannan bayanin ne ranar Talata a Sakkwato, inda yace “ ko wace cibiya daya daga cikin cibiyoyi na ciyar da mutane 200 zuwa 250 ne a rana.”

Kazalika, “a duk kwana goma ana kai buhun shinkafa 10, buhun gero 3, buhun wake 1 da kuma kuma buhun sikari guda. Tare da nama, kaji, kofuna, kwanon cin abinci da kuma kudi N10,000 zuwa ko wace cibiya dake jihar.” Inji Mallam Lawal.

Maidoki ya kara da cewa, “ Duba ga nasarar da cibiyar ta samu daga bara zuwa yanzu an samu karin sabbin cibiyoyin yayin da kasafin kudin wannan shirin nasu ya karu zuwa N380m.”

Kwamitin mu na bin diddigin abinda ke faruwa a dukkanin cibiyoyin domin ganin cewa babu almundahana ko halin rashin gaskiya a wadannan wurare.

Maidoki wanda shi ne shugaban kwamitin zakka da wakafi na jihar Sakkwato yace har ila yau babu wata tangarda da aka samu yayin gudanar da wannan shiri nasu.

A cewarsa duk wanda aka samu da hannu wurin aikata rashin gaskiya to zai fuskanci hukunci daidai da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel