EFCC ta titsiye jami’an gwamnatin Kwara akan bahallatsar N400m

EFCC ta titsiye jami’an gwamnatin Kwara akan bahallatsar N400m

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta sanar da kama wasu manyan jami’an gwamnatin jahar Kwara dana majalisar dokokin jahar Kwara bisa bahallatsar biyan wasu yan majalisu da yayan majalisar zartarwar jahar kimanin naira miliyan 400 babu aikin fari balle na baki.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin EFCC, Tony Orilade ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar daya fitar a ranar Laraba, 22 ga watan Mayu, inda yace ofishin EFCC dake garin Ilorin na jahar Kwara ne ya fara gudanar da wannan bincike.

KU KARANTA: Najeriya ta garkame ofisoshin jakadancinta a kasashe 4 saboda rashin kudi

EFCC ta titsiye jami’an gwamnatin Kwara akan bahallatsar N400m

EFCC ta titsiye jami’an gwamnatin Kwara akan bahallatsar N400m
Source: UGC

Sanarwar ta kara da cewa EFCC ta fara binciken ne daga sakataren gwamnatin jahar Kwara, Sola Gold da akawun majalisar dokokin jahar, Jummai Kperogi, wanda a yanzu haka suna hannun hukumar, inda EFCC ke zarginsu da sa hannu wajen sakin kudaden ba tare da bin ka’idojin aiki ba.

Kaakakin EFCC yace sun samu korafin cewa dukkanin yan majalisun dokokin jahar 25 da wasu kwamishinonin jahar sun karbi naira miliyan 400 a matsayin kudin sallama, duk kuwa da cewa ma’aikata na bin gwamnatin jahar bashin albashin watanni uku.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa hakkin yan majalisa da kwamishinonin ne samun kudin sallama, amma gwamnati mai zuwa ce ya kamata ta biyasu wadannan kudade ba gwamnatinsu ba, bugu da kari an biyasi kudin ne kafin karewar wa’adinsu.

Akawun majalisa, Jummai Kperogi ta bayyana ma EFCC cewa tabbas kowanne dan majalisa ya samu kudin sallamarsa, wanda ya kai kashi 200 na albashinsa, amma tace da amincewa gwamnan jahar Abdulfatah Ahmed aka biya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel