Hukumar jiragen sama ta kasa NCAA ta shiga yajin aiki na sai baba ta gani

Hukumar jiragen sama ta kasa NCAA ta shiga yajin aiki na sai baba ta gani

Hukumar jiragen sama ta kasa NCAA (Nigeria Civil Aviation Authority), ta ce a yau Laraba, 22, ga watan Mayun 2019 za ta tsunduma cikin yajin aiki na baba-ta-gani kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yajin aikin ya fara ne da misalin karfe 5.00 na safiyar ranar Laraba kamar yadda kungiyar ta bayar da sanarwar ankarar da daukacin al'ummar Najeriya cikin jawaban da fitar a ranar Talata da gabata.

Hukumar jiragen sama ta kasa NCAA ta shiga yajin aiki na sai baba ta gani

Hukumar jiragen sama ta kasa NCAA ta shiga yajin aiki na sai baba ta gani
Source: UGC

Majiyar jaridar Legit.ng kamar yadda hukumar NCAA ta bayyana ta ruwaito cewa, za a dirfafi yajin aikin gadan-gadan babu kakkautawa biyo bayan karewar wa'adi na kwanaki bakwai da hukumar da bai wa gwamnatin tarayya reshen ma'aikatar sufuri ta jiragen sama.

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar ta yi barazana dakile duk wata gudanar wa ta harkokin sufuri na jiragen sama a fadin kasar nan sakamakon rashin jin dadin shimfidar wasu tsare-tsare masu dakusar da kwazon ayyukan ta.

KARANTA KUMA: Buhari zai jagoranci zaman majalisar zantarwa na bankwana

Karamin ministan sufurin jiragen sama na kasa, Hadi Sirika, tu amakon da ya gabata ya mika kokon barar sa na neman kungiyar NCAA da ta zauna akan teburin sulhu domin warware takaddama ta rashin fahimtar juna dake tsakanin su a madadin hana ruwa gudu a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel