An shiga rudani yayinda kwamandan soji ya far ma ayarin mataimakin gwamnan Borno

An shiga rudani yayinda kwamandan soji ya far ma ayarin mataimakin gwamnan Borno

An samu banbancin ra’ayi tsakanin sojoji da yan sanda yayinda mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ke kaddamar da wasu ayyuka a Maiduguri, babbar birnin jihar Borno a ranar Talata, 21 ga watan Mayu.

Mataimakin shugaban kasar ya ziyarci Borno don kaddamar da wassu ayyukan gwamnatin Kashim Shettima mai barin gado.

Daga cikin ayyukan akwai makarantu, cibiyar GSM da kuma gini na yara yan gudun hijira a jihar.

Har ila yau, yayin da Osinbajo, Gwamna Kashim Shetima, da Usman Durkwa, mataimakin gwamna, suke kaddamar da wata makaranta a hanyar Bukumkutu a babban birnin jihar, jami’an tsaro masu hakkin kare su sun nuna banbanci ra’ayi a bainar jama’a.

An shiga rudani yayinda kwamandan soji ya far ma ayarin mataimakin gwamnan Borno

An shiga rudani yayinda kwamandan soji ya far ma ayarin mataimakin gwamnan Borno
Source: UGC

Rudani ya barke ne bayan Mike Alechenu, kwamandan sojojin Operation Lafiya Dole, ya hana ayarin motocin Durkawa hadewa da tawagan sauran manyan mutane.

Yayin da motar dake gaba a tawagar Durkawa ke kokarin motsawa, Alechenu yayi amfani da sandan dake hannunsa ya fasa gilashin motan.

Har ila yau yayi amfani da sandan wajen dukan direban farar motar kirar Hilux wanda ke dauke da jami’an tsaro kafin ya baiwa mutanensa umurnin sace iskan tayoyin motocin mataimakin gwamnoni da yayi kokarin motsawa.

Sojojin sun hada wukake da bindigogin su don bin umurnin da kwamandansu ya basu.

KU KARANTA KUMA: Masu zanga-zanga sun dauki gawawwaki 18 zuwa gidan gwamnati da fadar sarki

Achennu har ila yau yayi barazanar sanya ankwa ga hadimin Durkawa, mai mukamin ASP, wanda ya nemi a kwantar da hankula.

Saboda haka, yan sanda masu kananan mukamai sun rufe hanya yayin da suka gudanar da zanga zanga.

Har sai da hukumar tsaro na sirri suka shiga lamarin don magance lamarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel