Buhari zai jagoranci zaman majalisar zantarwa na bankwana

Buhari zai jagoranci zaman majalisar zantarwa na bankwana

A yau Laraba, 22 ga watan Mayun 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara jagorantar zaman majalisar zantarwa na bankwana yayin da ya rage saura mako guda a rantsar da shi a kan wani sabon wa'adi na jagorancin kasar nan tsawon shekaru 4 masu zuwa.

Majalisar zantarwa ta Najeriya da a turance a ke kiran ta da FEC (Federal Executive Council), ta kushin shugaban kasa, Mataimakin sa da kuma zababbun Ministoci da shugaban kasa ya rataya akalar jagorancin manyan ma'aikatun kasa.

Buhari zai jagoranci zaman majalisar zantarwa na bankwana

Buhari zai jagoranci zaman majalisar zantarwa na bankwana
Source: Facebook

Sauran 'yan majalisar sun hadar da sakataren gwamnatin tarayya, shugaban ma'aikatan gwamnati na kasa baki daya da kuma shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa.

Duba da tanadin sashe na 148 cikin kundin tsarin mulki, majalisar zantarwa za ta rika gudanar da zama a kowane mako domin tattaunawa akan yadda al'amurran kasa ke gudana a nan gida Najeriya da kuma wajen ta.

Baya ga haka kundin tsarin mulki ya shar'antawa majalisar zantarwa tabbatar da hadin kai da gwiwa tare da kasancewa tamkar tsintsiya madauri ta fuskar aiki a yayin sauke nauyin da rataya a wuyan shugaban kasa, mataimakin sa, da kuma Ministoci.

KARANTA KUMA: Rashin tsaro: An yi garkuwa da 'yan Najeriya 27 cikin kwanaki 2 a jihohi hudu

Kazalika majalisar zantarwa na da alhakin shawartar shugaban kasa akan kara kaimi wajen gudanar da muhimman ayyuka na yiwa kasa hidima bisa ga cancantar kujerar sa doriya akan wanda kundin tsarin mulki na kasa ya rataya a wuyan sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel