An damke wani da ya yi yunkurin shigar da wiwi cikin gidan yari a takalmi, hoto

An damke wani da ya yi yunkurin shigar da wiwi cikin gidan yari a takalmi, hoto

Hukumar Kula da Gidajen Yari (NPS) na babban birnin tarayya, Abuja ta kama wani Clement Jacob da laifin yunkurin safarar wani ganye da ake kyautata zaton wiwi ne zuwa cikin gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Kakakin hukumar, Chukwuedo Humphrey sanar da cewa wanda ke ake zargin mazaunin kauyen Deidei a Abuja ya boye ganyen wiwin ne a cikin takalminsa da ya ke shirin mikawa wani fursuna, Emeka Onyejikacki da ake tsare da shi saboda samun shi da muggan kwayoyi.

Humprey ya ce asirin wanda ake zargin ya tonu ne yayin da aka lura ya yi canjin takalmi da fursunan da ya zo ganawa da shi a lokacin da zai tafi.

Yadda wani matashi ya yi yunkurin shigar da tabar wiwi gidan yari

Yadda wani matashi ya yi yunkurin shigar da tabar wiwi gidan yari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kannywood: Ban durkusa domin bawa Nabruska hakuri ba - Hadiza Gabon

Ya ce, "Sufeta Hussain Ibrahim da ke kula da masu kawo ziyara ya lura anyi canjin takalmi cikin gaggawa hakan yasa ya bukaci a sake bincike bayan fursunan ya gama ganawa da wanda ya kai masa ziyara.

"A yayin binciken ne Sufeta Hussain ya bude sahun takalmin inda ya gano wasu ganye da aka boye a ciki.

"Da ya ke amsa tambayoyi, Jacob ya ce bai san abinda ke cikin takalmin ba inda ya ce wata Mrs Emeka ce umurci shi ya ziyarci Mr Emeka kuma suyi musayar takalmi kafin ya baro gidan yarin."

Humphery ya ce Kwantrollan NPS na Abuja, Mustapha Iliyasu Atta ya yabawa iya aiki na jami'in da ya gano wannan lamarin sannan ya tunatar da al'umma da wadanda 'yan uwansu ke tsare a gidan yari irin nauyin da ya rataya a kansu na tabbatar da cewa fursunonin sun sauya halayensu kafin su fito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel