Masu zanga-zanga sun dauki gawawwaki 18 zuwa gidan gwamnati da fadar sarki

Masu zanga-zanga sun dauki gawawwaki 18 zuwa gidan gwamnati da fadar sarki

Fusatattun matasa daga yankin karamar hukumar Batsari na jihar Katsina a jiya Litinin, 21 ga watan Mayu sun far ma gidan gwamnati da fadar sarkin Katsina dauke da gawawwakin mutane 18 da aka kashe a harin yan bindiga.

An kuma tattaro cewa yan bindiga sun kai hare-hare a kananan hukumomi uku na Jibia, Danmusa da kuma Faskari a jihar.

Masu zanga-zangar, wadanda suka kasance da yawa, sun tuka Babura da motoci biyar, inda suka zargi jami’an tsaro da aka tura yankinsu da gaza kare su. Sun kuma bayyana cewa yan bangan sa kai da ke yankin sun fi su yin kokari a yankin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rikicin ya fara ne a kauyen Yar Gamji da ke karamar hukumar Batsari lokacin da yan bindigan suka tuko babura suka kashe wasu manoma a safiyar ranar Talata yayinda suke kakkabe gonakinsu a shirinsu na shiga aikin noma bayan ruwan sama da aka kwarara cikin dare.

Al’umman sun ce sun nemi taimako amman babu jami’in tsaro da ya kawo agaji a lokacin.

Yan mintoci bayan lamarin ya auku, motar yan sanda ta iso kauyen, ta dauki gawawwakin wadanda aka kashe zuwa fadar mai garin Ruma. Wannan ya yiwa matasa a yankin zafi, wanda hakan yayi sanadiyar gudanar da zanga zanga.

Matasan sun daukaka zanga-zangar su zuwa reshen hedikwatar rundunar yan sanda dake yankin, wanda hakan ya tunzura yan sandan suk kore su, inda aka harbi mutane uku daga cikin masu zanga zangan.

Wannan ya cigaba da tayar da hankalin matasan kuma suka yanke shawaran kai gawawwakin babban birnin jihar yayinda suka cigaba da zanga zangar.

Yayin da yake magana a Gidan Gwamnati , kakakin masu zanga-zangar Aminu Runa yace sun dauki matakin ne don janyo hankula akan kisa da ake cigaba da kai wa kauyukansu sannan kuma suna bukatar a samar da ingantaccen tsaro daga yan bindiga.

Masu zanga-zanga sun dauki gawawwaki zuwa gidan gwamnati da fadar sarki

Masu zanga-zanga sun dauki gawawwaki zuwa gidan gwamnati da fadar sarki
Source: UGC

Yace ayyukan noma sun ja baya a yankunan kamar yanda mutane ke tsoron ziyartan gonakin su.

Gwamna Aminu Bello Masari yace gwamnatin sa tayi matukar damuwa da lamarin kashe kashe da yan bindiga ke daukakawa.

KU KARANTA KUMA: Rigima ya kaure a JUTH kan amfani da hijabi da ma’akata da dalibai mata ke yi

Har ila yau yayi kira ga masu zanga zangar dasu kwantar da hankali, ya bada tabbaci ga matasan cewa gwamnati tana matukar aiki don ganin ta magance lamarin.

A cewar shi, nadin da aka yi mishi kwanan nan a matsayin shugaban kwamitin tsaro na kungiyar gwamnonin arewa ya kasance mataki da zai kawo karshen ta’addanci.

Yayi kira ga al’umma da su nuna aminci ga hukumomin tsaro su kuma nuna tarayya da hadin kai dasu wajen yakan ta’addanci.

An fahimci cewa hare haren Jibia, Dan Musa da Faskari ne yayi sanadiyan kisan mutane da dama.

Mutane biyar ne aka rahoto an kashe a kauyen Mara Zamfara (Dan Musa) yayin da aka sace dabbobi da dama. Al’umman kauyen sun ce yan bindigan sun kai hare hare ga manoman dake aiki a gonaki. A Sabon Layin Galadima (Faskari), al’umma sunce mutane 11 na aka kashe.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel