Makonni uku kenan, babu labarin Magajin Garin Daura da aka sace

Makonni uku kenan, babu labarin Magajin Garin Daura da aka sace

Makonni uku kenan da wasu yan bindiga sukayi garkuwa da Magajin Garin Daura, alhaji Musa Umar, a gidansa dake Daura, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma har yanzu babu labarinsa.

Wasu yan bindiga hudu sunyi awon gaba da Magajin garin Dauran ne a a ranar 1 ga watan Mayu, 2019.

Yan bindigan sun dira garin Daura ne misalin karfe 7 na yamma, yayinda magajin garin ke dawowa daga Sallar Magariba.

Game da cewar mai idon shaida, masu garkuwa da mutanen sun shigo unguwar da mota kirar Peugeot 406 da Toyota Hilux suna harbin kan mai uwa da wabi. Kawai suka dauke Alhaji Umar, suka jefashi cikin motar kuma sumayi gaba da shi.

Har yanzu, babu labari kan halin da yake ciki, ba'a samu labarin abin masu garkuwa da mutanen ke bukata ba, hakazalika ba'a sani ko yana nan da rai ba.

Wata majiya na kusa iyalan Magajin garin sun bayyana cewa ana samun nasara kan ganin yadda za'a sakeashi amma iyalan sa jami'an tsaro sun ki jawabi kan abinda ake ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel